Labarin Wasanni: Nasarar Jamus kan Faransa
December 4, 2023A wasan karshen na cin kofin kwallon kafa na matasa 'yan kasa da shekaru 17 da haihuwa dai, Jamus din ta samu nasara a kan Faransa ne a bugun daga kai sai mai tsaron gida bayan an tashi a wasan biyu da biyu. A yayin bugun daga kai sai mai tsaron gidan, Jamus ta zura kwallaye hudu a raga yayin da Faransa ta zura kwallaye uku. Tun da farko a fafatawar neman matsayi na uku, kasar Mali ta doke Ajantina uku da nema.
A wasannin Bundesliga na Jamus din kuwa har yanzu kingiyar Bayern Munich za ta iya sake komawa kan terubin da Leverkuen da karbe da maki uku, bayan jinkirta wasan karshen mako da aka tsara tsakanin Bayern Munich din da Union Berlin sakamakon dusar kankara da ta mamaye birnin Munich din yayin da Leverkusen ta tashi kunnen doki daya da daya a gumurzunsu da Borusia Dortmund. Ita dai Leverkusen tana da maki 35 a yanzu, yayin da Bayern Munich ke da maki 32. A sauran wasannnin kuwa Bochum ta doke Wolfsburg da ci uku da daya, sannan Borussia Mochengladbad ta doke Hoffenheim da ci biyu da daya. Ita kuwa Freiburg ta bi Mainz har gida ta doke da ci daya mai ban haushi, kana RB Leipzig da doke Heidenheim da ci biyu da daya.
A wasannin Premier League da aka kara a Ingila kuwa, Newcastle United ta doke Manchester United da ci daya mai ban haushi kana Chelsea ta samu galaba a kan Brighton da ci uku da biyu. West Ham da Cristal Palacekuwa sun tashi wasa kunnen doki daya da daya, haka Mnchester City da Tottenham sun yi canjaras da ci uku da uku kamar yadda Bournemouth da Aston Villa suma suka yi canjaras amma biyu da biyu. Liverpool kuwa ta doke FC Fulham da ci hudu da uku, kana Arsenal ta doke Wolverhampton da ci biyu da daya. A La Ligar Spaniya kuwa, kungiyar Real Madrid ta samu galaba a kan Granada da ci biyu da nema haka Barcelona ta doke Atletiko Madrid da ci daya mai ban haushi. Osasuna da Real Sociedad sun tashi kunnen doki daya da daya, kamar yadda Sevilla da Villarreal suma suka tashi wasa daya da daya.
Kimanin mutane 20,340 suka hallara a birnin Mexiko na kasar Mexiko, domin ganin wasan Tennis tsakanin shahararren dan wasan Tennis na duniya Carlos Alcaraz ya da Tommy Paul. Shi kuwa shugaban hukumar kula da wasan guje-guje da tsalle-tsalle na duniya Thomas Bach ya sanar da shirye-shiryen wasanni da za a gudanar a shekara ta 2024 a birnin Paris na kasar Faransa da hukumar ke yi, domin karbar bakuncin wasannin Olympic na shekarar da ke tafen.