Labarin Wasanni: Nasarar Bayer Leverkusen
April 15, 2024zNasarar ta kungiyar Bayer 04 Leverkusen din dai, ta ba ta damar lashe kofin Bundesliga karo na farko a tarhinta a kakar wasanin ta bana wato 2023 zuwa 2024. Tun dai bayan da Borussia Dortmund ta lashe gasar ta Bundesliga a kakar wasanni ta 2011 zuwa 2012 Bayern Munich ta yi kaka gida tare da lashe gasar har karo 11 a jere, kofin da tawagar Xabi Alonso ta yi nasarar karya shi a bana. Wannan nasarar na zuwa ne bayan da ta lallasa kungiyar kwallon kafa ta Werder Bremen da ci biyar da nema. Godiya ga mai horas da 'yan wasa dan kasar Spaniya Xabi Alonso da ya jagorancin Leverkusen wajen lashe wanna kofi a mako na 29.
Tun farkon kakar wasannin ta bana Leverkusen ba ta yi rashin nasara a kowanne wasa ba, inda ta lashe wasanni 25 tare da yin kunne doki a hudu cikin wasanni 29 da suka fafata. Tuni dai kungiyar ta shiga cikin sawun kungiyoyin da suka buga wasanni sama da 40 ba tare da yin rashin nasara ba. Bayan lashe kofin zakarun Turai a shekara ta 1988 da kuma kofin kalubale na Jamus a 1993, wannan ne karo na farko da Bayer 04 din ta samu nasarar lashe wata gasa cikin shekaru 31 kana kuma kofi na uku a tarihinta. Filin wasa na BayArena da ke kan titin "Bismarckstraße" da a Lahadin karshen makon suka lankaya masa suna "Xabi-Alonso-Allee" ya dau harami, bayan nasarar lashe kofin Bundesliga da tawagar ta Alonso ta yi.
Kungiyar za kuma ta buga wasan karshe a na cin kofin kalubale na Jamus a nan gaba, inda za ta fafata da kungiyar kwallon kafa ta FC Kaiserslautern da ke rukuni na biyu na Bundesliga a ranar 25 ga watan Mayu mai zuwa. Haka kuma tana cikin kungiyoyin da suka kai ga wasan kusa da na kusa da na karshe wato quarter-finals a gasar cikin kofin kungiyoyin kasashen Turai wato Europa League. Kungiyoyin Bayern Munich da Stuttgart dai za su ci gaba da fafutukar neman maatsayi na biyu da na uku yayin da RB Leipzig da Borussia Dortmund ke kokawa a kan matsayi na hudu da na biyar. Ko wa zai samu nasara? Sauran wasanni biyar da ke tafe kafin kammala kakar ta bana za su nuna. A yanzu haka dai Bayer Leverkusen din ke kan gaba da maki 79, yayin da Bayern Munich da Stuttgart ke biye mata a matsayi na biyu da na uku dukansu da maki 63.
A gasar Premier League ta Ingila kuwa kungiyoyin Arsenal da Liverpool na shirin baras da damarsu ta samun nasarar a kakar wasannin ta bana, bayan da a karshen mako dukansu biyu suka barar da wasanninsu. Liverpool dai ta sha kashi a gida a hannun Crystal Palace da ci daya mai ban haushi, yayin da Aston Villa ma ta bi Arsenal har gida ta kuma caskarata da ci biyu da nema. Wannan dai ya bai wa Manchester City da a baya ke a matsayi na uku damar darewa kan teburin na Premier League, bayan da ta lallasa Luton Town da ci biyar da daya. A yanzu haka dai City din na da maki 73 a saman tebur, yayin da Arsenal da Liverpool ke biye mata a matsayi na biyu da na uku da maki 71 kowaccensu.
Ita kuwa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta ci gaba da rike kambunta na saman tebur a La liga kasar Spaniya, inda a yanzu maki takwas ne tsakaninta da Barcelona da ke a matsayi na biyu. Madrid din dai na saman tebur din ne da maki 78 kana Barcelona ke biye mata a matsayi na biyu da maki 70, sai kuma Girona da ta yi barazanar zama saman tebur na wani dan lokaci ke biye musu a matsayi na uku da maki 65.
Tawagar kungiyar kwallon kafa ta mata ta Najeriya Super Falcons ta samu nasrar zuwa gasar Olympics da kasar Faransa za ta karbi bakunci a birnin Paris da wasu birane shida na kasar, karo na farko a cikin shekaru 16 da kungiyar matan za ta sake halartar gasar. Shugaba Emmanuel Macron na Faransan dai, ya bayyana cewa a karon farko za a gudanar da bikin bude gasar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle a babban filin wasa na kasar maimakon filin river Seine da aka saba gudanar da bikin saboda dalilai na barazanar tsaro. Macron ya kuma ce za a takaita bikin a ginin Trocadero da ke tsallaken kogin daga Eiffel Tower ko ma mayar da shi zuwa filin wasan na "Stade de France".