Wasanni: Maroko ba ta halartar gasar CHAN
January 16, 2023Za mu dauko shirin daga Ingila inda a wasan Premier na karon battan gida, kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta doke Manchester City da 2 da 1, kana Chelsea ta lallasa Crystal Palace 1 mai ban haushi, sannan Arsenal ta yi tattaki har gida ta doke Tottenham 2 da 0, ita kuma Newcastle ta samu nasara kan Fulham 1 da nema.
Yanzu haka Arsenal ke jagorancin teburin na gasar Ingila da maki, 47, a matsayi na biyu kuwa akwai Manchester City da maki 39, kana a matsayi na uku akwai Newcastle mai maki 38, haka ita ma Manchester United na matsayi na hudu da maki 38, inda a matsayi na biyar akwai kuwa akwaiTottenham mai maki 33.
Takaddama tsakanin Aljeriya da Maroko a gasar CHAN
Yanzu ta tabbata cewa 'yan kasar Maroko zakarun kwallon kafa na kofin CHAN na nahiyar Afirka na kwallon da ya kunshi 'yan wasan da suke buga wasa a cikin gida ba za su halarci gasar da kasar Aljeriya za ta dauki nauyi ba, saboda kasar ta Aljeriya taki amincewa jirgin saman 'yan wasan da zai taso daga birnin Rabat fadar gwamnatin Maroko ya sauka kai tsaye a birnin Algiers, sakamakon katse huldar sufurin jirage sama tsakanin kasashe a watan Satumban shekara ta 2021 lokacin da dangantaka tsakanin kasashen biyu makwabta ta yi tsami. Tuni Gianni Infantino shugaban hukumar kula da wasan kwallon kafa ta FIFA da Patrice Motsepe shugaban hukumar kula da wasan kwallon kafa ta nahiyar Afirka suka fara neman hanyoyiyn sasanta wannan takaddama.
Wa ya haddasa mace-mace a filin wasan Indonesiya?
A kasar Indonesiya, an fara shari'ar mutane biyar da ake tuhuma da sakaci da ya kai ga mutuwar kimanin mutane 135 yayin da 'yan sanda suka watsa hayaki mai saka hawaye a filin wasan kwallon kafa, abin da ya haifar da tirmutsitsi a watan Oktoban shekarar da ta gabata ta 2022. Shi kansa Shugaba Joko Widodo na kasar na Indonesiya ya kafa kwamitin bincike sakamakon yadda lamarin ya fusata mutane a kasar. Akwai kimanin 'yan kallo 42,000 lokacin wasan kungiyoyin biyu masu hamayya da juna, a filin wasan da ya dace ya dauki kimanin mutane 36,000 kuma rige-rigen neman hanyar fita daga filin wasan lokacin da rikici ya kaure kuma 'yan sanda suka fara harba hayaki mai saka hawaye ya janyo mutuwar kimanin mutane 135. Wannan shi ne hadari a filin wasa mafi muni da aka taba samu a kasar ta Indonesiya.
Djokovic na halartar gasar tennis ta Ostareliya
Bayan da aka tasa keyarsa daga Ostareliya kuma aka hana shi karawa a gasar Tennis na watan Janairun bara, bayan da ya ce ba zai yi allurar rigakafin COVID-19 ba, Novak Djokovic ya dawo bana kuma ya bayyana farin-cikinsa na kasancewa a gasar, tunda a cewarsa ta na kayatar da shi. Sai dai ya ce ba zai taba mantawa da yadda aka tozarta shi ba. Gasar ta bana ta samu halartar manyan ‘yan wasan tennis na duniya.