1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bundesliga, Ronaldo a ManU, Messi ya yi wasan farko a PSG

Suleiman Babayo MNA
August 30, 2021

Cristiano Ronaldo a Manchester United, Lionel Messi a Paris St. Gemain, wasan Bundesliga da gasar Paralympics ta masu bukata ta musamman.

https://p.dw.com/p/3zgkD
Kombobild Cristiano Ronaldo und Leo Messi

Masu sauraro a ciki za a ji cewa shaharren dan wasa dan kasar Ajentina Lionel Messi ya yi fitowa ta farko a kungiyar PSG da ke Faransa, kana shi ma Cristiano Ronaldo na Potugal ya koma tsohuwar kungiyarsa ta Manchester United, sannan muna tafe da inda aka kwana a wasannin lig na Jamus wato Bundesliga gami da wasannin masu bukata ta musamman na guje-guje da tsalle-tsalle da ke wakana a birnin Tokyo na kasar Japan.

Cristiano Ronaldo ya sake komawa tsohuwar kungiyarsa ta Manchester United da ke Ingila, sakamakon barin Jeventus ta Italiya. Karkashin yarjejeniyar Ronaldo zai samu kimanin kudin Pound 480,000 kowane mako, a fisge sama da kudin Najeriya Naira milyan 300 duk mako.

A wasannin na Primiya lig na Ingila, kungiyar ta Manchester United ta bi Wolverhampton har gida ta doke ta da ci 1 mai ban haushi, ita kuma kungiyar Liverpool ta tashi 1 da 1 da kungiyar Chelsea, ko da yake an bai wa dan wasan Chelsea daya jan katin kora daga wasa. Sannan Manchester City ta wa Arsenal cin kacar tsohon keke rakacau, 5 da nema, kuma an bai wa dan wasan Arsenal jan katin kora.

Fitowar farko a jerin 'yan wasan kungiyar PSG ta Faransa

Shahararren dan wasan Ajentina, Lionel Messi ya yi fitowa ta farko a kungiyar Paris St. Gemain, inda kungiyar ta bi St. Reims har gida ta lallasa ta 2 da nema. Messi yana kan gaba da 'yan wasan da suka fi samun kudi a duniya kimanin kudin Euro dubu 729, wato kimanin kudin Najeriya, Naira milyan 370.

Bundesliga ta kayatar a wasannin mako na uku

Karawa tsakanin Bayern Munich da Hertha Berlin
Karawa tsakanin Bayern Munich da Hertha BerlinHoto: Matthias Hangst/Getty Images

A wasannin Bundesliga na Jamus, Dortmund ta doke Hoffenheim 3 da 2, yayin da Stuttgart ta bi Freiburg ta lallasa ta 3 da 2, ita ma FC Kolon ta doke Bochum 2 da 1, kana Leverkussen ta bi Augsburg gida ta doke ta 4 da 1, a nata bangaren Bayern Munich ta yi raga-raga da Hertha Berlin 5 da nema. Sannan Union Berlin ta doke Möchengladbach 2 da 1. Kuma Arminia Bielefeld da Eintracht Frankfurt sun tashi 1 da 1.

A nahiyar Afirka daga wannan Laraba ake fara karawa na wasannin tantance kasashen da za su wakilci nahiyar a gasar cin kofin kwallon kafa na duniya a shekara mai zuwa ta 2022 da kasar Katar za ta dauki nauyi. Senegal za ta kece raini da Togo, Mali da Ruwanda, kana Libiya da Gabon, ita kuma Guinea-Bissau da Guinea.

Ranar Alhamis Kenya za ta fafata da Yuganda, Jamhuriyar Nijar da Burkina Faso, Masar da Angola, kana Moroko da Sudan.

A ranar Jumma'a Najeriya za ta kece raini da kasar Laberiya, Kamaru da Malawi sannan Ghana da Habasha.

Gasar Paralympics a birnin Tokyo

Kwallon tenis a kan kekeken guragu a Tokyo, Japan
Kwallon tenis a kan kekeken guragu a Tokyo, JapanHoto: Issei Kato/REUTERS

A wasannin masu bukata ta musamman na guje-guje da tsalle-tsalle da ke wakana a birnin Tokyo na kasar Japan, China ke jagoranci teburin da zinare 53, azurfa 33, tagulla 30 a gaba daya tana da 116. Birtaniya tana matsayi na biyu da zinare 25, azurfa 19, da tagulla 20 a gaba daya tana da 64, sai Amirka a matsayi na uku da zinare 17, azurfa 17, da tagulla 11 a gaba daya tana da 45. Faransa tana matsayi na 13 da zinare 4, azurfa 7, da tagulla 16, a gaba daya tana da lambobi 27, inda Najeriya take matsayi na 21 a wannan jikon da zinare uku, azurfa 1 da tagulla 2 a gabya daya tana da 6. A wannan karon Jamus tana matsayi na 24 da zinare 2, azurfa 3, da tagulla 7 a gaba daya tana da 12.

Australiya tana mataki na 9 a yanzu haka a jerin kasashe masu mafi yawan lambobin wasannin Paralympics. A yanzu haka tana da lambobi 36, a ciki 8 zinari sai aurfa 15 da tagulla 13. Kaman takwarorinsu da suka yi gasar Olympic su ma ‘yan Paralympics sun kwashe lambobi sosai a ninkaya.