Senegal ta zama zakaran kwallon Afirka
February 7, 2022An kammala gasar cin kofin nahiyar Afirkan AFCON karo na 33 ne dai, tare da nasarar ta kasar Senegal a wasan karshe bayan doke Masar da ci hudu da biyu a bugun daga kai sai mai tsaron gida wato fenariti. Wannan ne dai karo na farko da Senegal ke lashe gasar, mafi muhimmanci a fagen wasannin Afirka. Bayan shan kashi sau biyu a wasan karshe a 2002 da 2019, a karshen dai 'yan wasan da Aliou Cissé ke horaswa sun samu nasara a bugun daga kai sai mai tsaron gida, sakamakon rashin zura kwallo a mintuna 90 na wannan wasa da 'yan wasan kasar Masar. Amma Senegal ce ta kasance mafi samun damar kai kora, lamarin da ya sa ta yin karo da golan Masar sau takwas. A karshe dai, Sadio Mané da ke bugawa a Liverpool ne ya zura kwallo ta karshe jim kadan bayan mai tsaron gidan Senegal wato Edouard Mendy ya kama bugun daga kai sai mai tsaron gidan da dan wasan Masar ya yi. Abin da ya sa aka tashi wasan Senegal na da ci hudu Masar kuma na da ci biyu.
Mai horas da 'yan wasan Senegal Aliou Cissé ya ce nasara Senegal na da nasaba da darasin da suka koya a wasan karshe na 2019 da suka yi da Algeria: "Ina ganin wadannan wasanni biyu ne dabam-dabam, a shekarar 2019 ban samu lokacin zama ba a lokacin da aka zura mana kwallo a raga. Don haka yanayin wasan ya canza gaba daya, mun ta kokarin farke kwallo da ake bin mu. Amma a yau ba irin wannan yanayi ba ne. Mun shirya wasan ta kowace siga, mun san cewa za mu iya yin nasara a cikin mintuna 90. Mun kuma san cewa za mu iya zuwa karin lokaci, amma kuma mun san cewa za mu iya yin nasara a bugun daga kai sai mai tsaron gida."
Fitaccen dan wasan Senegal din wato Sadio Mane bai boye farin cikinsa ba lokacin da ya lashe gwarzon dan wasan AFCON, lamarin da ke zama mahimmin mataki a rayuwarsa: "Wannan ita ce rana mafi mahimmanci a rayuwata. Kai ka ce mafarki, har yanzu ban yarda cewa mun lashe wnnan kofi ba. Mun dade muna jira, amma a yanz dukkanmu muna murna da alfaharin lashe wannan kofi. Na godewa dukkan 'yan Senegal, iyalina da abokaina da ma'aikata da daukacin tawagarmu. Mun sha wahala amma mun kai ga gaci."
Dubun-dubatar 'yan Senegal ne dai, suka kwana suna shagulgulan lashe kofin kwallon kafar Afirkan da tawagar kasarsu ta yi. Daliban jami'ar Cheikh Anta Diop da ke dakar na daga cikin wadanda suka dage wajen kallon wasan har zuwa bugun daga kai sai mai tsaron gida. Sai dai a nasu bangaren 'yan kasar Masar ba su ji da dadi ba, duk da cewa sau bakwai ne cikin tarihin kwallon kafar Afirkan suka dauki kofin. Amma kuma sun jinjinawa 'yan wasansu musamman ma Mohamed sahel dangane da namijin kokari da suka yi, inda suka ce sa a 'yan senegal suka ci amma ba su fi 'yan Masar wasa ba.
Kamaru mai masaukin baki ce ta kasance a matsayi na uku a gasar ta AFCON ta bana, duk da cewa da kyar da jibin goshi ta doke Burkina Faso a bugun fenarati. To daga kwallon maza a Afirka sai mu je ga na mata a wannan nahiya, inda 'yan kasa da shekaru 20 ke ci gaba da neman tikitin shiga gasar cin kofin duniya. Tawagar kwallon kafa ta mata 'yan kasa da shekaru 20 ta Najeriya Falconets, ta tsallake zuwa zagaye na gaba kuma na karshe na wasannin share fagen shiga gasar cin kofin duniya na mata da za ta gudana a kasar Costa Rica a watan Agustan wannan shekara ta 2022. Sun yi nasarar doke takwarorinsu na Kamaru da ci uku da nema zagaye na biyu da wannan rukuni da suka fafata a filin wasa na Moshood Abiola da ke Abuja. A Yanzu dai 'yan matan Falconets za su fafata ne da takwarorinsu na Senegal wadanda suka doke Morocco da ci biyar da uku a bugun fanariti.
A karshen mako an gudanar da wasannin mako 21 na kakar Bundesliga ta bana a Jamus, kuma nasarar da Bayern Munich ta samu nasara da ci uku da biyu akan takwararta ta RB Leipzig, ta ba ta damar ci gaba da yi wa Dortmund rata bayan da Bayer Leverkusen ta bi Borussia Dortmund din har gida ta kuma doke ta da ci biyar da biyu. A sauran muhimman wasannin karshen mako kuwa, Union Berlin ta fadi a gaban Augsburg da ci biyu da nema, amma ta ci gaba da rike matsayinta na hudu a teburin Bundesliga da zai iya sa ta cancantar shiga gasar zakarun Turai. Ita kuwa Cologne ta doke Freiburg da ci daya mai ban haushi. A kasan teburi kuwa Wolfsburg ta yi wa kungiyar Greuther Fürth kaca-kaca da ci hudu da daya, wanda hakan ya ba ta damar hayewa zuwa mataki na 12.
Kwanaki uku bayan fara wasannin guje-guje da tsalle-tsalle a lokacin sanyi a birnin Beijing na Chaina kasar Sweden ce ta kasance a kan gaba, inda a yanzu take da lambobin zinare uku. Ita kuwa Rasha tana biya mata baya da lambobi biyu na zinare biyu na azurfa biyu na tagulla, yayin da Noway ke a matsayi na uku. Ita kuwa Jamus tana matsayi na biyar da lambar zinare daya da azurfa daya. Sai dai babu dan Afirka ko daya da ya nuna bajinta a wasannin na lokacin sanyi. Dama ana daukar 'yan wasan Afirka da suka shiga gasar Olympics ta lokacin sanyi a matsayin abin almara. Amma 'yan wasa shida daga kasashe biyar dabam-dabam na halartar gasar da birnin Beijing ke daukar bakunci, ciki har da dan Najeriya daya da dan Ghana daya da dan Iritiriiya daya da 'yan Madagaska biyu da kuma dan Maroko daya.