Wasanni: Tuchel ya maye gurbin Nagelsmann
March 29, 2023Thomas Tuchel ya fara aiki a matsayin sabon mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich da ke Jamus, gabanin wasan lig na Bundesliga ta ranar Asabar inda Bayern Munich za ta fafata da Dortmund. A baya dai Tuchel ya horas da kungiyar Chelsea da ke Ingila, kuma jami'an kungiyar ta Bayern Munich suna fata ya farfado da ita daga matsayi na biyu a teburin Bundesliga na Jamus, domin komawa matsayin farko da ta saba babakere, inda yanzu kungiyar da za su kara wato Dortmund ta karbe matsayin farko na teburin, bayan da ya maye gurbin Julian Nagelsmann wanda ake gani kungiyar ta fara sako-sako karkashin jagorancinsa.
Jagoran 'yan wasan kasar Ingila, Harry Kane ya shaida wa Firaminista Rishi Sunak na Birtaniya cewa yana fatan zama mutumin da ya fi kowa jefa kwallaye a raga a gasar Premier Lig. Kane ya fadi haka bayan saka kwallo na 54 a raga cikin wasanni 81 da ya yi wa Ingila wasa, inda suka samu nasara kan kasar Italiya da ci 2 da 1 a wasan neman zuwa gasar cin kofin kwallon kafa ta kasashen Turai ta shekarar 2024, inda ya zarce Wayne Rooney wajen jefa kwallaye a raga a tawagar Ingila. Kuma yanzu yana da muradin zarce kowa a gasar Premier Lig, wajen zarce Alan Shearer da ya jefa kwallaye 260, kuma mafi yawa a tsawon tarihi.
A wasannin neman zuwa gasar cin kofin kwallon kafa ta Afirka, Najeriya ta gamu da rashin nasara a gida bayan Guinea Bissau ta yi mata ci daya mai ban haushi.
Nelson Piquet zakaran kambun tseren motoci na Formula One, dan kasar Brazil ya biya kudi kimanin milyan tara, kwatankwancin Dala milyan daya, wanda aka ci tararsa saboda amfani da kalaman nuna wariyar launin fata. Wata kotu da ke kasar ta Brazil ta same Nelson Piquet da laifin sakamakon kalaman a shekara ta 2021, da ya yi wa Lewis Hamilton jagoran tagowar motoci na Mercedes.
Garcia Leon 'yar kasar Peru ta kafa sabon tarihin tafiya da kafa na kilo-mita 35, wanda ta gama cikin sa'oi biyu da mintuna 37 da kuma dakika 44 a Dudince, da ke kasar Slovakiya. An dade wadda ta yi kusa da haka ita ce Klavdiya Afanasyeva 'yar kasar Rasha a shekara ta 2019, a wannan gasar motsa jiki da ke cikin masu tasiri a wasannin guje-guje da tsalle na duniya.
Kana an dakatar da Imane Khelif 'yar wasan dambe 'yar kasar Aljeriya daga wasa sa'oi gabanin wasan damben duniya na mata a birnin New Delhi na kasar Indiya, saboda hukumar kula da wasan damba ta duniya ta gano cewa 'yar damben ba ta cika ka'idojin kasashen dunyia ba.
Ita dai Imane Khelif mai shekaru 23 da haihuwa, tun farko an tsara za ta kara wasan karshe da 'yar China na cin zinare, kuma yanzu wadda ita 'yar kasar Aljeriya ta samu galaba a kanta ce daga kasar Thailand ta yi wasan na karshe. Wannan dakatarwa na ci gaba da haifar da cece-kuce da zarge-zarge a kafofin yada labaran kasra ta Aljeriya.