Duniyar wasanni a bara da kuma bana
January 2, 2023Abubuwa da dama dai sun faru a duniyar wasanni a shekarar da ta gabata, inda tun daga farkon shekarar bayan da Rasha ta kaddamar da yaki a Ukraine hukumomin wasanni dabam-dabam suka daga mata jan kati ta hanyar dakatar da ita daga wasanni da dama. Duk da cewa an yi ta cece-kuce kan dacewa da kuma rashin dacewar hakan, inda wasu ke ganin cewa bai kamata a saka siyasa a harkar wasanni ba yayin da wasu kuma ke ganin hakan ya yi daidai domin Moscow ta cancanci hukunci. Duk da wannan cece-kuce dai, har kawo yanzu Rashan na fuskantar takunkumi a fannin wasannin.
Wani abu da ya sake daukar hankali shi ne gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya da aka gudanar a kasar Katar, inda Moroko ta bayar da mamamki bayan da ta zamo kasar Afirka ta farko da ta kai ga wasan kusa da na karshe wato "Semi Finals". Duk da cewa ba ta samu nasarar tsallake wannan zagaye ba, amma ta kafa tarihi a wasan kawllon kafa a duniya. Baya ga wannan kuma sai nasarar da Ajantina ta samu ta daukar kofin, bayan lallasa Faransa a bugun daga kai sai mai tsaron gida. Nasarar dai ta bai wa shahararren dan wasan kwallon kafa na kasar ta Ajantina wato Lionel Messi damar daukar kofin duniya a karon farko, kuma a wasansa na karshe a gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya.
A kance ana bikin duniya ake na kiyama, wani babban al'amari da ya shafi duniyar kwallon kafa a shekarar da ta gabata shi ne rashin shahararren dan wasan kwallon kafar nan na duniya wato Pele da ya kwanta dama yana da shekaru 82 a duniya. An haifi marigayi Edson Arantes do Nascimento da aka fi sani da Pele a ranar 23 ga watan Oktobar shekarar 1940 a Tres Coracoes, Brazil. A shekarar 1956 Pele ya samu kwantiragi da kungiyar Santos ta Brazil, kuma ya zura kwallo a ragar St. Andre a wasansa na farko a gasar lig yana da shekaru 15. Ba da dadewa ba, aka kira shi zuwa tawagar kasar Brazil. Yana da shekaru 16 da kwanaki 257 kacal ya buga wasansa na farko a duniya a wasan da suka doke Argentina da cibiyu da daya, inda ya zura kwallo daya tilo da ta bai wa Brazil damar lashe wasan. Shekara daya bayan nan a gasar cin kofin duniya a Sweden, ya kasance a tawagar 'yan wasan Brazil. Duk da cewa ya yi zaman benci a farko, amma ya zura kwallaye shida a wasanni hudu kacal.
Labarin da aka bude wannan shekara ta 2023 da shi kuwa, shi ne na kwantiragin da shahararren dan wasan kasar Potugal Cristiano Ronaldo ya sanya hannu a kai, ta makudan kudi a Saudiyya. Tsohon dan wasan kungiyar Manchester United da suka raba gari dutse a hannun riga, ya sanya hannu kan sabuwar kwantiragi da kungiyar Al-Nassr ta Saudiyya. Rahotanni sun nunar da cewa Ronaldo zai rinka daukar dalar Amirka miliyan 75 duk shekara, a kwantiragin ta tsawon shekaru biyu da rabi.
A gasar Premier League ta Ingila kuwa ga dukkan alamu kungiyar Arsenal da ke saman tebur ta sha alwashin daukar kofin na bana, ganin yadda take ci gaba da yi wa Manchester City da ke biye mata a matsayi na biyu nisa. A yanzu haka dai Arsenal din na da maki 43 ne bayan da ta lallasa Brighton da ci hudu da biyu, yayin da City din ke da maki 36 bayan da ta tashi wasanta da Everton kunnen doki daya da daya a karshen mako. Koda yake akwai sauran tafiya, ganin cewa gasar ba ta zo karshe ba. Wata kungiya da gasar ta bana ke mata ba dadi dai ita ce Liverpool, inda a yanzu haka take a matsyi na shida a kan teburin na Premier League.