1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harkokin motsa jiki na mako

Lateefa Mustapha Ja'afar
November 8, 2021

Shahararren dan wasan kokawar nan na Amirka mai asalin da Najeriya Kamaru Usman ya ci gaba da rike kambunsa, bayan nasarar lallasa Colby Covington a karshen mako.

https://p.dw.com/p/42jKZ
UFC I Kamaru Usman I  Mixed martial artist
Hoto: Mike Mastrandrea/ZUMA/picture alliance

 Biyo bayan wannan nasarar, a yanzu haka Usman ke kan gaba sakamakon lashe wasanni 19 a jere. Da yake zantawa da manema Labarai jim kadan bayan samun wannan nasara tasa, Usman ya ce:

"Kamar yadda na fada masa, ya kamata ka san cewa a wannan lokaci da muke ciki, kwararre ne kai amma akwai wanda ya fi ka kwarewa. Hana shi katabus tun daga farkon wasan zuwa karhse, abin jin dadi ne".

A karshen makon nan ne aka kammala wasan karshe na gasar kwallon Tennis mai taken "Kano Hard court" a filin wasa na Kano club da ke birnin Kano, gasar da aka gabatar kashi na 34 taNajariya ta kayatar matuka bayan da aka sami matasa da suka taka rawa wajen cin nasara a gasar.

Fußball Bundesliga Bayern München - SC Freiburg
Bayern München na wasa da FreiburgHoto: Sven Hoppe/dpa/picture alliance

Bari kuma mu fada fagen kwallon kafa, inda a karshen makon aka fafata a mako na 11 na kakar wasannin kungiyoyin kwallon kafa na Jamus ta bana wato Bundesliga. An dai tashi kunne doki daya da daya a wasan da aka fafafata atsakanin kungiyar kwalllon kafa ta Mainz da Mönchengladbach, yayin da Bayern Munich ta lallasa Freiburg da ci biyu da daya. Ita kuwa Stuttgart ta sha kashi ne a gida a hannun Armenia Bielefeld da ci daya mai ban haushi. Ita ma Wolfsburg ta lallasa Augsburg da ci daya mai ban haushi, yayin da Dortmund ta barar da wasanta a ziyarar da ta kai wa kungiyar kwallon kafa ta RB Leipzig da ci biyu da daya. 

Bundesliga 1. FC Köln v 1. FC Union Berlin | Tor Grischa Prömel
Wasan Cologne da BerlinHoto: Revierfoto/imago images

A wasannin da aka fafata jiya Lahadi kuwa, an tashi wasa kunnen doki daya da daya tsakanin Hertha Berlin da Leverkussen yayin da Cologne da Unioin Berlin suka tashi wasa canjaras biyu da biyu, ita kuwa kutal Greuther Fürth ta sha kashi a hannun Eintracht Frankfurt da ci biyu da daya. Har yanzu dai Bayern ce ke kan gaba a teburin na Bundesliga da maki 28 yayin da Dortmind ke biye mata a matsayi na biyu da maki 24 sai kuma Freiburg a matsayi na uku da maki 22.