1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wasannin Olympics a London sun kammala

August 13, 2012

An bayyana gasar Olympics ta 2012 a birnin London da wanda ya samu babbar nasara.

https://p.dw.com/p/15on0
Hoto: dapd

Ga ɗaukacin mazauna birnin na London da baƙi maziyarta, gasar ta kasance ɗaya daga cikin wasannin Olympics da suka fi ƙayatarwa. Mohammad Nasiru Awal na ɗauke da ƙarin bayani.

"Tun a lokacin shirye shiryen ɗaukar baƙoncin gasar Olympics ɗin a birnin London 'yan Birtaniya sun yi ta ƙorafi game da kuɗin da aka kashe tare da saka ayar tambaya ko gasar za ta yi armashi. Sai dai an yaba da ƙasaitaccen bikin buɗe wasannin a ciki da wajen ƙasar ta Birtaniya. Ba kowa ne kuma zai manta fitowar da sarauniyar Ingila ta yi tare da James Bond a matsayin wata 'yar wasan kwaikwayo ba."

Cikin ƙiftawa da bismilla wasannin motsa jikin suka fara burge 'yan Birtaniya, amma jama'a sun fusata domin wasu wuraren wasa sun kasance wayam a farko-farko wasannin yayin da dubban mutane suka kasa samun tikitin shiga kallon wasannin. Mai tseren keke na tawagar Birtaniya Geraint Thomas ya ce su ma kansu 'yan wasan sun ji takaicin hakan. Yace:

"Gaskiya abin baƙin ciki ne ganin babu kowa a wasu wuraren zama a zauren gasar ninƙaya da ɗaukar nauyi. Bin san dalili ba, amma an samu mutane da yawa a waje da suka so shiga kallon wasannin. Da kamata yayi su ci gajiyar wannan dama."

Waɗanda suka shiyar gasar ta London sun ce ya zama wajibi a bar wasu kujeru ga dangin masu wasa, jami'ai, 'yan jarida da masu tallafawa, amma sun jinginar da wannan damar kuma daga baya ƙorafin ya kwanta lokacin da wasannin suka yi nisa.

Olympische Sommerspiele 2012 in London Abschluß Feier Brasilien Flagge
Tutar Olympics da aka mikawa birnin Rio de Jeneiro na BrazilHoto: picture-alliance/dpa

Wata matslar kuma ita ce yadda a wasu lokutan harkar kasuwanci ta tashi daga tsakiyar London zuwa gabacin birnin inda dandalin wasan yake. Arthur Rason ɗan kasuwa ne a tsakiyar London. Yace:

"Na yi farin ciki da Ingila ta ɗauki nauyin shirya wasannin Olympics, domin abu ne mai kyau a gare mu. Bai dame ni. Abin da ya dameni shi ne rashin ciniki a nan wurin."

Sai dai wasu ƙungiyoyin 'yan kasuwa sun ce rashin cinikin na gajeren lokaci kuma nan gaba za a ga fa'idojin shirya gasar musamman a fannin yawon buɗe ido. Ga dai ra'ayoyin wasu baƙi da suka halarci gasar.

London 2012 5000 Meter Frauen
Yar Habasha Meseret Defar da ta ci zinariya a tseren 5000Hoto: Getty Images

"Ko da ma mutane na sha'awar zuwa London, amma a kwanakin nan mun ga abubuwa masu ban sha'awa. Daga Norway nake, gasar ta ƙayatar."

"London ta burge mu. Akwai mutane ko-ina. Abin yayi kyau ƙwarai da gaske."

Kafofin yaɗa labaru na ƙetare ma sun yaba da gasar inda mujallar Der Speigel ta Jamus ta kira gasar da cewa sun yi armashi, ita kuma jaridar USA Today ta ce an mayar da London zuwa wurin fara'a na masu aikin sa kai na Olympics, nagartaccen tsarin sufuri da 'yan kallo masu farin ciki da annashuwa.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Umaru Aliyu