1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wasu motocin bus sun yi hadari a Masar

August 22, 2014

Akalla mutane fiye da talatin ne suka rasu yayin da wasu kuma 40 suka jikata, sakamakon wani karo da motocin bus-bus guda biyu sukayi a Kudancin kasar Masar.

https://p.dw.com/p/1CzA6
Hoto: Reuters

Rahotanni daga birnin Alkahira na Masar, na cewa a kalla mutane 33 suka rasu sakamakon wani hadarin motocin bus-bus guda biyu da sukayi karo da juna, a yankin Sinai dake Kudancin kasar ta Masar.

Hadarin ya faru ne da sanyin safiyar yau din nan a cewar kanfanin dillancin labaran kasar na Mena, inda ya kara da cewa, an samu a kalla mutane 40 da suka jikkata sakamakon hadarin,kuma 'yan asalin kasashen daban-daban da suka hada da 'yan kasar Rasha, Yamal, da kuma Saudiya, kuma ana ci gaba da fitar da gawawaki, inda ake tsammanin adadin wadanda suka rasun zai iya karuwa.

Dama dai 'yan kasar ta Masar na kokawa a kullu yaumin da matsalolin rishin kyawon hanyoyi dake haddasa hadarurruka da dama a wannan kasa.

Mawallafi: Salisou Boukari
Edita : Umaru Aliyu