1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turai sun je nuna goyon bayansu ga Ukraine

Abdul-raheem Hassan
March 15, 2022

Yayin da ake neman shawo kan rikicin Rasha da Ukraine, wasu kasashen kungiyar NATO sun nuna goyon baya ga Ukraine bayan da sojojin Moscow suka kashe mutane da dama a yunkurin dannawa Kyiv babban birnin kasar Ukiraine.

https://p.dw.com/p/48VpH
Brüssel | Sitzung Europaparlament zur Ukraine
Hoto: John Thys/AFP/Getty Images

Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da ministocin kasashen jamhuriyar Chek da Poland da Sulobeniya suka nufi babban birnin Ukraine din ta jirgin kasa don nuna goyoyn bayansu ga Ukraine. Shugabannin sun shirya ganawa da Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy da Firaiminista Denys Shmyhal a Kyiv inda ake sa ran kasashen Turan za su gabatar da nasu tallafin.

Gwamnatin Ukraine ta ayyana dokar hana fita na sao'i 35 a babban birin kasar yayin da dakarun Rasha ke cigaba da barin wuta, duk da cewa shugaban kasar ya kirayi sojojin Rasha su mika wuya. Yanzu haka kungiyoyin agaji na kokawa kan yadda dubban fararen hula ke rufe ba tare da abinci ba.