Watan Ramadan: Azumi a lokacin corona
Musulmai na gudanar da azumin Ramadan a karo na biyu a cikin corona. Hotuna daga sassan duniya!
Indonesiya: Ziyarar makabarta
Al'ummar kasar na ziyarar makabarta a daidai lokacin da suke shirin tarbar watan Ramadan.
Indiya: Haduwa ta yanar gizo
A birnin New Delhi, wata mata ce ke waya da ‘yan uwanta, a bayanta hoton babban masallacin Jama ne da a baya sama da mutum dubu ke buda baki a ciki.
Saudiyya: Sallar Taraweeh a Mekka
Al'umma na gudanar da sallar Taraweeh a masallacin Ka’aba. A farkon watan Afirilu ne mahukunta na kasar Saudiyya suka ba da damar bude masallacin ga al'ummar da suka yi rigakafin corona domin gudanar da ayyukan Umrah.
Malesiya: Salla da takunkumin rufe baki da hanci
Mata sanye da takunkumi suna sallah a ranar farko ta watan Ramadan a birnin Kuala Lampur. An sassauta dokar corona domin gudanar da ibada a watan da ma bude kasuwanni dukka karkashin matakan kariya na corona.
Siriya: Yara na karatun Al-Kur'ani
A cikin babban masallacin Umayyad da ke Damascus. Wannan masallacin na daga cikin masallatan farko a duniya kuma a wannan wata na Ramadan dubban ‘yan kasar ne ke hallartar sallar Taraweeh a cikinsa. A karon farko a shekarar da ta gabata an rufe masallacin saboda annobar corona.
Najeriya: Shan ruwa cikin farin ciki
A masallacin Al-Habibiyyah da ke Abuja, yara na buda baki a ranar farko ta watan Ramadan. Yaran da ba su kai ga balaga ba azumin Ramadan bai zama dole a kansu ba amma a lokuta da dama su kan zabi yin azumin tare da sauran mutanen gidansu.
Afganistan: Abinci ga mabukata
Abincin shan ruwa ga mutane mabukata manya da yara a birnin Kandahar. Watan Ramadan lokaci ne da ake son yawaita yin sadaka. Duk da matsalar da annobar corona ta jefa mutane ciki, ana gudanar da iftar musamman ga marasa karfi.
Masar: Bude Masallatai
Mutane na gudanar da sallar Taraweeh a masallacin Al-Azhar. A shekarar da ta gabata an rufe masallatai a fadin kasar amma a yanzu an bude domin gudanar da ibada a wannan wata na Ramadan karkashin matakan kariya na cutar corona.