1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Aung San Suu Kyi ta yi watsi da zargin cin zarafi

Abdoulaye Mamane Amadou
December 11, 2019

Shugaba Aung San Suu Kyi ta kasar Myanmar ta ki amincewa da dukkannin zargin cin zarafi da kisan kiyashi kan musulmai marasa rinjaye 'yan kabilar Rohingya a kasar.

https://p.dw.com/p/3UbcY
Niederlande Den Haag Aung San Suu Kyi vor dem Internationalen Gerichtshof
Hoto: picture-alliance/AP Photo/P. Dejong

Da ta ke kare kanta da sojojin kasar a yayin shari'ar kwanaki uku da aka fara jiya a gaban kotun ICC da ke birnin Heague, Aung San Suu Kyi ta sheda wa kotun cewa samame da dakarun kasar suka kai a shekarar 2017 yammacin jahar Rakhine, samame ne na dakile ta'addanci bayan zargin mayakan Rohingya da kai hari kan ofisohin 'yan sanda, kana ta kuma kara da cewa zargin kisan kiyashin ba shi da tuhsen da bai ma kamata kotun ta ICC ma ta saurari shari'ar ba.

A watan Nuwamban da ya shige ne kasar Gambiya ta shigar da kara a gaban kotun duniya tana mai kalubalantar gwamnatin Myanmar kan zargin kisan kiyashi kan musulmai marasa rinjaye a jihar Rakhine.