Wadatar abinciNa duniya
WFP na jan hankali kan barazanar 'yunwa
September 12, 2023Talla
Hukumar WFP da ke da mazauni a birnin Rome ta koka kan yadda ake samun karuwar bukatun abinci a duniya, yayin da take fuskantar gibin kudade na sama da kashi 60 cikin 100, wanda ke zama mafi girma a tarihinta. Hukumar ta abinci ta kara da cewa , duk wani mataki na rage kashi 1% na tallafin na barazanar jefa mutane 400,000 cikin halin rashin abinci.
Karin bayani: karancin abinci ya sa Nijar
Kiyasi ya nunar da cewa mutane miliyan 40 na fuskantar matsalar yunwa a kasashen Afghanistan da Siriya da Somaliya da Haiti sakamakon tsuke bakin aljuhu da WFP ta yi.