1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

WHO: An kakkabe cutar Maleriya a Cape Verde

Abdullahi Tanko Bala
January 12, 2024

Cape Verde ta zama kasa ta uku a Afirka da suka yi nasarar kawar da cutar zazzabin cizon sauro ta hanyar ingantaccen tsarin yaki da cutar a fadin kasar

https://p.dw.com/p/4bBkF
Malaria-Bekämpfung in Afrika | Kenia | Impfstoff Mosquirix
Hoto: Brian ONGORO/AFP

Kungiyar lafiya ta duniya WHO ta sanar da kawo karshen cutar zazzabin cizon sauro na Malaria a kasar Cape Verde, inda ta zama kasa ta uku a cikin kasashen Afrika da suka yi nasarar kawar da cutar.

Sauran kasashen da aka kakkabe cutar sun hada da Mauritius wadda ta yi nasarar kawar da cutar a 1973 da kuma Algeria da ita ma ta kawo karshen cutar a shekarar 2009.

Kasar Cape Verde dai ta sha fama da annoba da dama kafin daga bisani ta dauki muhimmin matakin kasa baki daya da ya mayar da hankali kan bayar da magani da kuma binciken cutar a dukkan matakai.

Domin dakile cutar hukumomi sun kaddamar da bayar da magani kyauta ga matafiya da 'yan gudun hijira.