WHO: Barazanar ciwon suga a Afirka
November 12, 2021Talla
A wani binciken farko da hukumar ta gudanar a kasashen Afirka 13 ya gano ana samun mutuwar kashi 10 na masu ciwon suga sanadiyar annobar Covid-19 idan aka kwatanta da kashi biyu kacal da ke mutuwa sanadiyar annobar a tsakanin sauran mutane.
Alkaluma na nuni da cewa kimanin mutane miliyan 24 a nahiyar ke fama da cutar diabetes, inda ake hasashen ta yiwu adadin ya karu zuwa miliyan 55 nan da shekarar 2045.
Hukumar ta WHO ta ce babban abin damuwa ne kimanin kashi 70 cikin 100 na mutanen nahiyar ba su da masaniyar suna dauke da cutar. Ana dai ganin samun yawan masu dauke da cutar a Afirka na da alaka da yadda ake fama da matsalar rashin cin abinci mai gina jiki saboda matsin rayuwa.