1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

W.H.O: Corona na ta'azzara lafiyar duniya

June 2, 2020

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta ce annobar corona ta zama babbar barazana ga sauran mutane masu fama da wasu larurori na kiwon lafiya a fadin duniya.

https://p.dw.com/p/3d7qO
Schweiz PK WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus zu Coronavirus
Hoto: picture-alliance/Keystone/S. Di Nolfi

A wani binciken da ta gudanar cikin kasashen duniya 155 a watan jiya, hukumar lafiyar ta MDD, ta ce mutane da dama da ke fama da manyan matsaloli na lafiya da ke kan hadarin fuskantar illar corona musamman su ne abin ya fi shafa.

Hakan kuwa na faruwa ne saboda rashin kulawa da ta kamata su samu a wannan lokaci da hankali ya koma kan yaki da wannan annoba.

Binciken ya gano cewa an dakatar da kulawa da masu cutuka da ke da nasaba da zuciya da kashi 31%, haka su ma masu fama da cutar daji ko Cancer da suka kai kashi 42% hakan ya shafe su.

sakamakon binciken ya ce su ma masu fama da cutar sikari ko Diabetes da suka kai 49% ba sa samun kulawa saboda annobar, kamar yadda wadanda ke bukatar kulawar gaggawa da suka kai 31% da ke a cikin adadin.