1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

WHO ta ce Afirka ta fi fama da malaria

Mouhamadou Awal BalarabeApril 23, 2015

Hukumar lafiya ta Duniya ta ce mutane rabin miliyan ne ke fama da zazzabin cizon sauro a duniya a duk shekara, akasarinsu mazauna nahiyar Afirka musmman ma yara.

https://p.dw.com/p/1FDZt
Hoto: Getty Images/Fred Dufour

Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana cewa mutane 500,000 ne ke rasa rayukansu a kowace shekara sakamakon kamuwa da zazzabin cizon sauro, duk kuma da matakan da ake dauka don dakile wannan cuta a duniya. A lokacin wani taron manaima labarai da ta gudanar gabanin ranar yakin da malariar, WHO ko kuma OMS ta ce kashi 90% na wadannan suke harbuwa da Malariar na da zama ne a nahiyar Afirka. Ta kuma kara da cewa cutar ta fi salwantar da rayukansu yara kanana.

Tuni ma dai WHO ko OMS ta fitar da wani sabon tsarin yaki da Malaria wanda za ta kadamar a watan Mayu mai zuwa. A kasashe masu tasowa dai kashi daya bisa biyar na yaran da suka harbu da malaria ne ke samun magani, yayin da su ma mata masu juna biyu miliyan 15 suke samun kansu a cikin wannan hali na rashi magani.