1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

WHO: Coronavirus na kara yaduwa

July 14, 2020

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta bayyana damuwarta dangane da yadda annobar cutar COVID-19 ke kara yaduwa a duniya da kuma yadda gwamnatoci ke sakaci wajen daukar matakan da suka dace.

https://p.dw.com/p/3fInY
Tedros Adhanom Ghebreyesus
Shugaban Hukumatr Lafiya ta Duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus Hoto: Getty Images/Afp/F. Coffrini

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya nuna damuwarsa a kan yadda masu dauke da cutar ke karuwa a fadin duniya, wanda sababbin alkaluma suka nuna cewa cutar ta halaka sama da mutane dubu 570 daga cikin mutane kimanin miliyan 13 da suka kamu. Hukumar ta yi kiran daukar matakan kariya, wanda ta ce idan ba haka ba wannan cutar za ta ci gaba da dagula al'amuran yau da kullum. Bayar da tazara tsakanin mutane da yawaita wanke hannu da yin tari a gwiwar hannu da ma zama a gida idan mutum ya fara jin jikinsa ba daidai ba, na daga cikin abubuwan da al'umma za su kiyaye, a cewar Ghebreyesus: "Idan har ba a kiyaye wadannan ka'idojin ba, to tabbas wannan cutar za ta ci gaba da yaduwa fiye da yadda muke tunani."

China Peking Mobile Coronavirus-Teststation
Coronavirus ta fara bulla a ChainaHoto: picture-alliance/Xinhua/J. Huanzong

Tun bayan bullar annobar cutar ta coronavirus a kasar Chaina a shekarar da ta gabata ta 2019, yanzu haka yawan sababbin kamuwa da cutar ya haura mutane dubu 230 a kowacce rana. Kasashe da dama musamman ma a nahiyar Turai, sun nuna cewar da akwai yiwuwar kawo karshen cutar. Shugaban Hukumar ta Lafiya ya kuma bayyana mahimmancin gaggauta daukar matakan yaki da cutar ba tare da bata lokaci ba. A jawabin da ya yiwa manema labarai a ranar Litinin din da ta gabata a taron da hukumar ta yi a birnin Geneva na kasar Switzerland, Ghebreyesus ya bukaci mutane su zauna cikin shirin ko ta kwana, yana mai cewa babu tabbacin lokacin da wannan annoba za ta kare.

A nashi bangaren, babban jami'in shirin gaggawa na hukumar ta WHO Mark Ryan ya ce dole ne al'umma su nemi hanyar da za su rayu da wannan cutar, ya kara da cewar maganar kawo karshenta a cikin 'yan watanni ba abu ne mai yiwuuwa ba. Har ya zuwa yanzu dai babu takamaiman maganin da hukumar ta amince da shi wanda za a iya cewa yana warkar da cutar. Kasashen duniya dai na ci gaba da gwada basirar su wajen ganin an sami magani da ma rigakafin wannan cutar da ta zame wa duniya karfen kafa.