WHO ta koka kan yanayin kiwon lafiya a jihar Borno
January 10, 2017Wannan sabon rahoto na hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya wato WHO a takaice ya alakanta lalacewar cibiyoyin kiwon lafiya da tabarbarewar tsaro a jihar ta Borno, wanda ya haifar da karancin jami'an kiwon lafiya da na'urorin aikin asibiti da karancin magunguna. Haka kuma rahoton ya alakanta wannan matsalar rashin nagargatattun kayayyakin more rayuwa, kamar ruwa da makamashin wutar lantarki, lamarin da ya yi matukar shafar ayyukan ceton rai na yawancin yankunan da matsalar tsaro ya shafa.
A cewar Dr. Wondi Alemu jami'in hukumar lafiya a Najeriya, wannan rahoton ya gano akwai ciboyoyin lafiya guda 743 a jihar Borno, inda aka rusa kashi 35% kashi 29% kuma aka lalata wani bangaren su, saura kashi 36% ne kawai ba abinda ya taba su.
Daga cikin wadan suka saura ba a lalata ba kuma kashi daya cikin su ne ke da isassun kayan aiki, kamar yadda wannan rahoto ya nuna.
A cewar Baba Umar, wani jami'in kiwon lafiya da ya fito daga karamar hukumar Kukawa, akwai gaskiya a wannan rahoto kuma ya kamata gwamnati ta dauki matakai na gyara wannan matsalol, saboda muhimmancin da lafiya ta ke da shi.
A ziyarar da wakilin DW ya kai asibitin kwararru na Maiduguri babban birnin jihar ta Borno, da wasu asibotici da cibiyoyin lafiya da ke cikin kwaryar birnin Maiduguri, ya ga mutane da dama a layukan ganin likita kuma yawancin ma'aikatana na fadi tashin ganin sun biya bukatun masu neman lafiyar.
Wakilin na DW ya yi tattaki zuwa hukumar kula da asibitoci ta jihar Borno, inda babban daraktan ta Dr. Salihu Kwayambura ya shaida masa cewa lallai an lalata cibiyoyin lafiya, amma gwamnati ta dauki matakin gyara da kuma daukar ma'aikata musamman likitoci da kuma samar da kayayyaki a asibitocin.
Rahoton na WHO ya nuna cewa yanzu haka, akwai cibiyoyin lafiya kimanin 100 da aka samar kuma 49 daga cikin na kai dauki ne ga wadan suka tsere daga matsugunun su, da ke zaune a sansanonin 'yan gudun hijira a kewayen birnin Maiduguri.