WHO ta soki kasashen da ke siye rigakafin corona
January 19, 2021Talla
Tedros Adhanom Ghebreyesus ya yi gargadin cewa rashin rarraba allurar rigakafin coronavirus ga kasashe masu fama da talauci da kasashe masu arziki ke yi ka iya tsawaita lokacin annobar, inda ya soki kasashen masu arziki da siyewa da kuma tara rigakafin da ake da su a halin yanzu.
Kazalika ya kuma ce kasashe masu arziki za su kasance cikin hadari idan har suka yi biris da kasashe masu fama da talauci.
Ghebreyesus, ya ce a halin yanzu shirye-shiryen fara isar da allurar rigakafin cutar a watan Fabrairu ga yawancin kasashen da ke fama da talauci a duniya na fuskantar kalubale.
A makon da ya gabata dai jami'ar Johns Hopkins ta ce mutanen da suka mutu sanadiyar annobar sun haura mutum miliyan biyau a duniya.