WHO ta yi gargadi kan fesa magani a tituna
May 16, 2020Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ko OMS ta yi gargadin cewa matakin da kasashe suke dauka na fesa magani a saman tituna da kasuwanni da ma a kan mutane da nufin kashe kwayoyin cutar Covid 19 babban hadari ne ga lafiyar jama'a.
A wani littafi da ta wallafa a wannan Asabar kan muhimmanci tsarkake wurare da nufin kashe kwayoyin cutar Corona, Hukumar Lafiyar ta Duniya ta ce babu tabbacin cewa yadda ake bada maganin na yin tasiri wajen kashe kwayoyin cutar ta Covid 19 wacce ya zuwa yanzu ta kashe mutane sama da dubu 300 a duniya.
Kazalika hukumar ta WHO ta tituna ba nan ne matattarar kwayoyin cutar ba, sannan magungunan da ake fesawa wadanda na kemestri ne na da hadari ga lafiyar Dan Adam, kuma ba sa hana mutuman da ya harbi da cutar ya ci gaba da yada ta ga jama'a ta hanyar dafawa ko tsattsafar yawun da ke fita daga bakinsa a loakcin magana.