COVID-19: Kalubalen da ke gaban WHO
May 18, 2020Kwanaki biyu kacal Hukumar Lafiyar ta Duniya (WHO) za ta shafe tana wannan taro maimakon kwanaki shida zuwa 10 da ta saba a shekarun baya. Hasali ma baya ga nazarin al'amuran yau da kullum na kiwon lafiya, mahalartan za su mayar da hankali ne baki daya kan matsala daya tilo da ta addabi duniya wato annobar COVID-19. Ya zuwa yanzu dai, ba wanda zai iya tantancewa ko mayar da hankali kan yaduwar cutar numfashin ta haifar wa WHO da wasu matsaloli a fannin kiwon lafiya a duniya.
Kalubale mai yawa
Amma hukumar ta WHO za ta shiga mawuyacin hali idan kamar yadda ta yi barazana a watannin da suka wuce, Amirka ta daina bayar da kason kudin da ta saba ba ta. A kasafin shekara ta 2018 zuwa 19, Amirkan ta bayar da sama da kaso 14 cikin 100 na kudin da kasashen duniya suka saba bai wa WHO. Suerie Moon babbar jami'i a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Global Health Center at the graduate Institute of Geneva ta ce ba karamar illa ce ke tattare da tsame hannun Amirka a WHO ba, duba da cewa wannan kasa na tallafawa ainin a yaki da ake yi da cutar Polio a duniya. Moon ta ce matakin zai mayar da hannun agogo baya, a kokarin da ake yi na rabuwa kwata-kwata da Polio a doron kasa.
Gwamnatin Amirka ta nuna alamar karkatowa, inda a karshen mako tashar talabijin ta Fox News ta ruwaito cewa ta amince ta zuba wa Hukumar Lafiya ta Duniyar kason kudi daidai da na Chaina, ma'ana dalar Amirkan miliyan 57 da dubu 400 a shekara ta 2020. Amma gaskiyar maganar ita ce, ya zuwa 30 ga watan Afrilu, 2020, Chaina da Amirka ba su biya kason kudinsu ga WHO na wannan shekarar ba. Kasar Jamus ga misali ta biya rabin kudin da ya kamata ta zuba ne kawai, yayin da ita ma Amirka ba ta biya dukkan kudin da ke kanta ba sabanin kasar Chaina.
Amirka ta yi amai ta lashe
Amma me ya sa Amirka ta yi amai ta lashe game da gudummawar kudi da take bai wa WHO? Suerie Moon uerie Moon, babbar jami'a a Cibiyar Global Health Center at the graduate Institute of Geneva ta ce, hakan ba ya rasa nasaba da raunin da kasar ke samu a fannin karfin fada a ji. Shugaba Trump na Amirkan ya bayyana cewa Chaina tana da tasiri sosai a Hukumar Lafiya ta Duniya, lamarin da ya sa WHO yin rufa-rufa kan yadda Chaina ta yaki cutar. Tuni Hukumar ta karyata. Sai dai Trump na da na shi laifin, saboda ya nuna shakku kan ta'adin da cutar coronavirus ka iya yi ga rayuwar dan Adam. Amma kuma a halin yanzu WHO na sara tana duba bakin gatari, saboda ba ta son tunzura kasashen biyu da suke sahun farko na masu samar mata da kudin gudanar da ayyukanta.