WikiLeaks: Assange ya yi nasara ta wucin gadi kan Amurka
March 26, 2024Babbar kotun ta ce wajibi a Amirka ta tattabar cewa ba za ta yanke masa hukuncin kisa ba idan aka mikashi domin fuskantar hukunci.
Karin Bayani: Assange ya yi nasarar daukaka kara
An dai shafe kusan shekaru 10 ana kai ruwa rana kan shari'ar, Assange wanda a yanzu yake da shekaru shekaru 52 yana fuskantar tuhume-ruhume 18 dangane da cin amanar kasa bayan da ya wallafa bayanan sirrin sojin Amirka a kasashen Iraki da Afhanistan.
Karin Bayani: Za a cigaba da shari'ar Assange a Birtaniya
An fara sanin shafin na WikiLeaks kusan shekaru 13 da suka gabata bayan ya bankado labarin wani jirgin shelikwaftar Amurka da ya hallaka mutane da dama a birnin Bagadaza na kasar Iraqi ciki har da ma'aikatan kamfanin dillancin labarai na Reuters. Julian Assange ya shafe lokaci mai tsawo a cikin ofishin jakadancin Ecuador a Burtaniya.