WTO: A wadata duniya da rigakafin corona
May 6, 2021Talla
Sabuwar shugabar kungiyar kasuwanci ta duniya WTO Ngozi Okonjo-Iweala ta yi kira da a hau teburin tattaunawa domin tsara yadda za a wadata kasashen duniya da alluran rigakafin COVID-19 ba tare da nuna fifiko ko wariya ba. Shugabar ta yi wannan kiran ne a wajen babban taron kungiyar, inda ta ce ta haka ne kawai za a iya yakar cutar bai daya domin a gudu tare a kuma tsira tare.
Batun na wadata duniya da rigakafin da alama ya samu karbuwa a wajen taron, bayan da wakilan kasashe arba'in mambobin kungiyar WTO da suka gudanar da jawabai, sun kara da cewa baya ga samun wadatar rigakafin, ya kuma cancanta a kara ingancinta tare da rarraba ta lunguna da sakuna na fadin duniya.