Wurare tara da ba a zaton samunsu a birnin Berlin
Berlin babban birnin Jamus tun bayan sake hadewar kasar a 3 ga watan Oktoban 1990, birni ne da ke alfahari da manyan gine-gine na tarihi, amma kuma akwai wasu wurare da kawo yanzu ko mazauna birnin ba su san da su ba.
Gabar teku da ke kewaye da rerayi
Akwai teku iri-iri a birnin, mafi shahara shi ne gidan cin abinci na Lido da ke a gabar tekun Wannsee, mutum akalla dubu 50 ka iya shakatawa a wannan wuri. Yana da tsayin mita 1,200 wato kafa 3,937. Cikin nishadi mai shakatawa ka iya mancewa, yana birnin Berlin. Wannan ba ya rasa nasaba da kyaun yashin tekun da ke hade da nau'in yashin tekun yankin Baltic.
Nau'in furanni mai kama da nau'in furen Cherry na kasar Japan
A kan iyakar birnin na Berlin da Lichterfelde da birnin Teltow, nau'in furannin Cherry kusan dubu biyu ke budewa. Kai ka ce daga kasar Japan aka yi odarsu. Amma ba mamaki don kuwa a lokacin bikin murnar faduwar bangon Berlin a 1989, wata kafar talabijin ta Japan ta samar da tallafin da aka yi amfani da kudaden siyo nau'in furen na Cherry.
Dawisu launi dabam-dabam na nishadantar da masu yawon bude ido
Akwai damar yin nishadi a wannan yankin da ake da tarin dawisu a Havel, bai da nisa daga tekun Lido na Wannsee. Ana da dawisu masu tarin yawa da ke yawonsu suna walawa a wannan wuri mai suna Pfaueninsel da Sarkin Prussiya Friedrich Wilhelm II ya samar. Ya kasance daya daga cikin wurare masu muhimmanci na UNESCO da masu yawon bude ido ke yawan sintiri.
Bauna a gandun dajin savanna
Ana da kimanin bauna 13 a gandun dajin Pfaueninsel da ke kan hanyar ruwan Tegeler Fliess a gefen birnin Berlin. Ba a bukatar noma ciyawa a gandun dajin don suna tattake su, suna kuma kayatar da masu yawon bude ido sosai. An kwaso su daga cikin birni inda yanzu haka ake ajiye da su a wannan wuri da ke kayatar da baki a birnin na Berlin.
Rayuwa kamar a karkara
Ga masu sha'awar hawa tsauni a gabar ruwan Tegeler Fliess, akwai bukatar mutum ya soma tattaki ta Alt-Lübars. Garin Reinickendorf shi ne kauye mafi dadewa a Berlin, har ya zuwa yanzu manoma na tasiri. A kewaye yake da daji a wani yanayi mai cike da ni'ima duk da haka kauyen ba shi da nisa daga birnin Berlin don kuwa mintuna 30 kadai ya raba su da birnin.
Mota mai lilo tamkar a yankin Alps
Berlin ba ta da tsaunuka kamar na yankin Alps, amma akwai wadannan kananan motocin da aka kirkira a shekarar 2017, yana kai kawo ya zuwa gabashin yankin Marzahn. Daga cikin motocin da ke lilon shida daga ciki na da tagogi na gilashi da zai bai wa mai yawon bude ido damar ganin komai daga can kololuwa, kama daga lambuna da ke kunshe da nau'ukan furanni daga kasashen duniya.
Lamari mai kama da almara na shirin fim
Yawo a yankin Plänterwald zai saka ka ji tamkar kamar kana cikin shirin fim na Jurassic Park kashi na biyu. A wannan dakin tarihin na Berlin da ke gabar ruwan Spree, za ka iya ganin jirgi mai dauke da fatalwa da sauran abubuwan al'ajabi. Suna da kayatarwa amma babu zahiri cikin abubuwan don duk ajiyar tarihi aka yi amma yanzu wurin ya koma kufai tun daga shekarar 2002. Ana shirin gyara.
Wurin bauta na Indiyawa
Kwalliya da kaloli sun mamaye wurin bauta na Hindu mai suna Sri Ganesha. Yana yankin Volkspark Hasenheide a Neukölln. Tun daga shekarar 2009 aka soma aikin gyara ana fatan gudanar da bikin bude wurin a watan Oktobar 2020. Sadaukarwa ce ga giwar da ake bautawa ta Ganesha, da ake alakantawa da sa'a da kaifin ilimi da basira da arziki.
Rayuwa a karkashin ruwa
A yankin tsakiyar Berlin ana iya ganin wannan hasumiyar akwatin kifaye na ruwan AquaDom, shi ne mafi girma a duniya. Yanzu haka ana kan gyara, amma nan ba da jimawa ba baki masu yawon bude ido, za su iya shiga hasumiyar don yin kallo, inda suke iya ganin nau'ukan kifaye sama da dubu daya da dari biyar.