1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ya ya ake zaben shugaban kasa a Amurka?

October 22, 2024

A yayin da zaben shugaban kasar Amurka ke kara karatowa, al'umma da dama na tambayoyi kan wasu muhimman bayanai da suka shafi zaben na ranar 5 ga watan Nuwamban 2024.

https://p.dw.com/p/4m6aD
Donald Trump da Kamala Harris
Hoto: DW

Ana sa ran zaben zai yi zafi ne tsakanin 'yar takarar jam'iyyar Democrats Kamala Harris da kuma Donald Trump na jam'iyyar Republican. Batu na farko da za mu duba shi ne shin wanene zai iya tsayawa takarar shugabancin Amurka?

Donald Trump da Kamala Harris
Hoto: Andrew Caballero-Reynolds/AFP/Getty Image | Alex Wong/Getty Images

Duk mai sha'awar shiga takarar shugabancin Amurka dole sai ya kasance haifaffen kasar wanda ya kai akalla shekara 35 da haihuwa kuma ya zauna a cikin kasar har na tsawon shekara 14 idan ba soja bane.

Abu na biyu kuwa shi ne abubuwa da dan takara ke bukata kafun shiga takara

To a kan wannan kam dai bari in mika ku ga Farfesan kimiyyar siyasa Wayne Steger na jami'ar DePaul University a jihar Illinois da ke cewa hatta wadanda suka taba zaman gidan kaso ma suna da damar shiga zabe.

Zaben Amurka na 2024 Trump da Harris
Hoto: Alex Brandon/AP Photo/picture alliance

"Kusan ko wane dan kasa da ya kai shekarun tsayawa takara zai iya shiga zaben shugabn kasa takaice ma, wannan nanan cikin kundin tsarin mulkin Amurka. Za a iya tuhumarka da laifi amma kuma ka tsaya takara. Tanadi ne na kundin tsarin mulkinmu domin a bai wa wadanda aka taba tuhuma dama su yi jagoranci.

To me yake faruwa a zaben na shugaban kasa?

Amsar itace abu mai sauki, bayan manyan tarukan jam'iyyun Democrats da Republican da ke zama alamar kada gangar siyasa, sai yakin neman zabe ya fara zafi. A ranar zabe kuma, miliyoyin 'yan kasa da suka yi rijistar kada kuri'a za su je dangwala wa wanda ya kwanta musu a rai a birane da kauyukan Amurka.

Abu na karshe mai sarkakiya da za mu duba shi ne  kwamitin masu zaɓe da ake kira Electoral College.

Muhawarar yakin neman zabe Trump da Harris
Hoto: Lindsey Wasson/AP Photo/picture alliance

Ba kuri'un da mutane ke kadawa kadai bane ne dai za su bai wa dan takarar shugabancin Amurka nasara, a'a,  kwamitin masu zaɓe da ake kira Electoral College ne ke da wuka da nama kan wanda zai shugabanci kasar, kuma kwamitin ya kunshi mutum 538 ne. Idan dan takara ya samu kuri'u 270 na mambobin wannan kwamitin to shikenan ya haye.

Ana dai duba girman kasa da kuma yawan mutane ne wajen daukar mambobin kwamitin na electoral College.