1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tasirin nahiyar Afirka ga sabuwar gwamnatin Jamus

Abdourahamane Hassane RGB
November 29, 2021

Masana sun soma sharhi kan irin gajiyar da kasashen nahiyar Afirka za su iya ci daga sabuwar gwamnatin kawancen Jamus da ke shirin karbar ragamar mulki.

https://p.dw.com/p/43d6P
Deutschland Symbolbild Koalition
Hoto: Torsten Sukrow/Sulupress/picture alliance

Manyan Jam'iyyun siyasa na Jamus da suka kula kawance a makon jiya domin kafa gwamnati a nan gaba watau SDP da Green da kuma FDP  sun bayyana manofinsu na cikin gida da waje a tsawon shekaru hudu na mulkin da za su yi. Sau hudu kawancen jam'iyyun ke ambato sunan Afirka a cikin yarjejeniyar da suka cimma, sabanin yadda tsohon kawance da ya jagorancigwamnati tsakanin masu ra'ayin 'yan mazan jiya na jam'iyyar Angela Merkel da kuma Social Democrat masu ra'ayin sauyi wanda a lokacin sau uku kawai suka ambato Afirka a cikin tsohuwar yarjejeniyar kawancen. Karin Bayani: Jamus na son karin masana'antu a Afirka

Deutschland Berlin | Konferenz Compact with Africa | Angela Merkel, Bundeskanzlerin | Gruppenbild
Angela Merkel tare da wasu shagabanin AfirkaHoto: Reuters/F. Bensch

Amma masani kana kwararre a kan nahiyar Afirka Robert Kappel ya ce babu alamun sabon kawancen na jam'iyyun siyasar zai bai wa Afirka fifiko.."Idan aka kwatanta da yarjejeniyar haɗin gwiwar ta 2017, manufofin a kan  Afirka  batun ne da ba ya cikin tsakiyar damuwar kasar, ko da shi ke ma tsohuwar gwamnatin ta yi iya nata kokari akwai tambayoyi da ake azawa akan batu na manufofin kan Afirka da Turai da ma harkokin cikin gida da wannan sabon kawancen''

Idan ba a manta ba, Jam'iyyar masu fafutukar kare muhalli Green  na son ganin na bayar da tallafi na kudade wajen shirin yaki da dumamar yanayi a nahiyar Afirka. A taikace dai gaba ɗaya sabuwar yarjejeniyar ta ƙunshi mafi yawan abubuwan da aka riga aka yi a tsofuwar gwamnatin. karin hadin gwiwa da Tarayyar Afirka da karin taimako ga yankin Sahel da ke fuskantar matsalar ta'addanci.

A bangaran fuskar cinikayya, za a ci gaba da huldar tattalin arziki a tsarin nan na ''Compact with Afirka''. Sai dai babu batun zuba hanayen jari na kamfanonin da masana'antu mallarka gwamnatin Jamus a Afirka. Matakin da ke zama abin taikaici a cewar Christoph Kannengießer, wani masani na tattalin arziki. ''Ina tsammanin kawancen idan yana son ci gaba sai yayi kazar-kazar na kara karfafa hulda da Afirka domin kula cikakkiyar hulda musammun a cikin hanyar manufofin kungiyar tarrayar Turai''

A karshe a kan batun 'yan cirani, yarjejeniyar tsakanin manyan jam'iyyu siyasar na Jamus da ke shirin kafa gwamnati hadaka ta tanadi bin hanyoyin da suka dace, kafin shigowa jamus. Amma dai sun ce akwai yi yuwar kula wata yarjejeniya ta musammun a kan batu a tsakanin Jamus da kasashen Najeriya da Ghana.