Yadda ake fama da zafi a nahiyar Turai
Nahiyar Turai ta shiga tsananin yanayi na zafi, inda ake ganin gobara a dazuka. Birane da sauran wurare na neman hanyoyin samun sanyi. Wane mataki ne na gajere da kuma dogon zango da zai samar da sa'ida?
Gobarar daji mai tsanani
Gobarar daji ta yi muni a tsibirin Gran Canaria na kasar Spain. Akalla akwai jami'an kashe gobara 300 tare da manyan jirage da ma na helikofta na kashe gobarar da ke kai komon ganin sun shawo kan wutar. Akwai kimanin gidajen kwana 11 da suka kone kurmus. Zafin bazara ya afka wa kasashen Turai fiye da yadda aka zata. Yayin da alkaluman yanayin zafin ke karuwa, haka hadarin gobara ma ke karuwa.
Yadda wuta ke ta'adi a Girka
Gobarar kurmi da ta sauran dazuka na cinye yankuna da dama a Girka ciki har da a Athens babban birni. Cikin hanzari wutar ta cinye busassun wurare sannan ta bazu zuwa Anavyssos mai yawan al'uma a yankin Attica. Haka ma abin yake a yankin tekun Lagonisi da Saronida inda jama'a ke zuwa shakatawa. A nan ne ake da gidajen sauke baki masu yawon bude ido wadanda ke kai ziyara a wannan lokaci na shekara.
Kokarin kare zafin rana
Nan wani mutum ne a birnin Rome na kasar Italiya ke kare zafin rana da karamar rigarsa. Manyan garuruwa masu gine-ginen kankare da ba su da bishiyoyi, su ne suka fi fama da zafi. Amma kuma akwai wasu matakai da suke taimakawa wajen samun sanyi da ba sai lallai an dogara da kare rana da riguna ba.
Birane masu matakai a Jamus
Wannan gini mai koren yanayi a birnin Düsseldorf na kasar Jamus, ya tanadi dabarar kyautata yanayi a wajen. Nan gaba lallai ne dukkanin birane da jihohi na kasar Jamus su fitar da hanyoyin kare kansu daga illolin sauyin yanayi. Ba da jimawa ba ne ma gwamnati a Berlin ta amince da daftarin daukar matakan a kasa baki daya. Galibin biranen da ma suna da karancin bishiyoyi da ciyayi yadda ya kamata.
Yadda ake mararin samun yayyafin sama
Wannan yarinya ce karama a birnin Krakow na kasar Poland ke wasa a wata farfajiyar wurin shakatawa da ke feso ruwa. Tuni wasu biranen kasar suka samar da wuraren sama wa mutane sanyi ta amfani da na'urori masu feshi. Sai dai kuma a kasashe kamar Italiya, ana fama kuma da karancin ruwa. Don haka kula da wadannan na'urori na wuya.
Ko'ina fari fat
Mutanen kasar Girka na amfani da tsari mai kyau na samar da sanyi. Fararen gidaje kamar wadannan na birnin Astypalea, ba su tsaya ga kawata su kadai ba - suna ma kare radadin zafi saboda yadda haskensu ke dacewa da na rana. Sai dai ba ko'ina ne ke iya bin tsarin a nahiyar Turai ba saboda dokokin da suka shafi tsarin gine-gine da kula da gidaje.
Shinge na tafi-da-gidanka!
A kasar Switzerland, mutane na kirkirar hanyoyin inganta yanayi ta hanyar amfani da koren tsirrai. A nan shinge ne da ake iya motsawa aka samar a birnin Basel. Ana ganin ya dace da tsarin kula da yanayi na wannan birni. An ware kudaden samar da irin wadannan shingaye da yawansu ya kai miliyan 9.4 million na kudin kasar, wato kwatankwacin Euro miliyan 9.7 ko dalar Amurka miliyan 10.1.
Tuna dabbobi da ruwan sha
Samun cibiyoyin samar da ruwan sha muhimmin mataki ne na rage zafi a garuruwa. Ana ganin irin wadannan cibiyoyi na kyauta da ke a birnin Frankfurt na Jamus da wasu kbiranen Turai da dama suka kyaikwaya. Dabbobi irin Karnuka na more wannan tsari a lokaci na zafi. Daga cikin watan Agustan 2022, gwamnatin Jamus ta sanya kafa wuraren samar da tsaftataccen ruwa a inda jama'a ke haduwa zama wajibi.
Ko zai dace a koma wa hadarin kimiyya?
Akwai dabaru kyawawa a fagen kimiyyar yanayi a zamanin yau. Guda daga ciki shi ne yadda ake amfani da fasaha wajen samar da hadari a ilimance. Akasari ana gamuwa da matsalolin samun tururi da iskar da ke taimaka wa samun hadari na asali. Don haka ne ilimin kimiyya ya bullo tukwanen da ke tafasa tare da sauya ruwan teku zuwa tururi da kan zama hadari a karshe. Ko hakan na iya yin amfani a gaba?