1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yadda rikicin diflomasiyya da Katar zai shafi Afirka

Salissou Boukari
June 8, 2017

Bayan da Saudiyya da wasu kasashe suka dauki matakin katse huldar diflomasiyyar da kasar Katar, masu sharhi a Afirka sun soma tofa albarkacin bakinsu kan yadda matakin zai shafi kasashen na Afirka.

https://p.dw.com/p/2eKnW
Katar Außenminister
Ministan harkokin wajen kasar Katar Mohammed bin Abdulrahman Al-ThaniHoto: Getty Images/AFP/K. Jaafar

Har ya zuwa farkon shekarun 2000 daga nahiyar Afirka, kasashen yankin Magreb da Mauritaniya da Sudan da Eritriya ne kadai ke da huldar diflomasiyya da kasar Katar wacce Allah ya huwace mata arzikin man fetir da kuma musamman iskar Gas. Amma a shekaru goma na baya-bayan nan kasashen Afirka kimanin 20 ne da suka hada da kamar Najeriya da Afirka ta Kudu da Kenya da Senegal da Laberiya da Benin da Jamhuriyar Nijar suka kulla huldar diflomasiyya da kasar ta Katar, inda tuni wasun su suka bude ofishin jakadancinsu a birnin Doha da kwadayin samun masu zuwa zuba jari a kasashensu ko sayen iskar gas a farashi mai rahusa. Docta Ngarlem Tolde Evariste masanin ilimin kimiyyar siyasa da tattalin arziki a jami'ar birnin Ndjamena na kasar Chadi ya ce hakan ka iya yin munmunan tasiri ga kasashen na Afirka:

Makomar huldar kasashen Afrika da Katar

Katar Treffen erdölfördernder Länder
Lokacin da Ministan Mai na Tarayyar Najeriya Emmanuel Ibe Kachikwu ya je taro a Katar.Hoto: picture-alliance/dpa

"Katar ta shigo nahiyar Afirka ne a fannin gudanar da ayyukan jin kai, inda take aiko da tawagar likitoci da samar da magunguna ga al'umma tare kuma da tallafa wa kungiyoyi masu zaman kansu da ke aikin kyautata rayuwar al'umma. Dan haka ko abin bai shafi gwamnatoci kai tsaye ba, to akwai yiwuwar su kungiyoyi masu zaman kansu su ji a jikinsu."

To sai dai wasu manazarta a nahiyar ta Afirka yabawa suka yi da matakin na wasu kasashe na katse huldar diflomasiyya da kasar ta Katar. Fakaba Sissoko daraktan cibiyar bincike kan harkokin siyasa tattalin arziki da zamantakewa ta kasar Mali na daga cikin masu wannan goyon baya. Sai dai kuma ya ce matakin diflomasiyyar kadai ba zai wadatar ba wajen shawo kan matsalar tsaron da ake fuskanta a yankin Sahel:

"A yau ba kasar Katar ba ce kadai ke daukar nauyin kungiyoyin 'yan ta'adda. Babban kuskure ne tunanin cewa da zaran an dauki matakin tattalin arziki kan Katar an ci nasarar yaki da ta'addanci . Kamata ya yi a duba rawar da wasu manyan kasashen duniya suke takawa cikin yada ta'addanci. Kuma ya kamata 'yan Afirka su daina tunanin daga waje ne za a iya shawo masu kan matsalar ta'addanci da suke fama da ita."

Katar Emir Scheich Tamim bin Hamad Al-Thani
Sarkin kasar Katar Sheik Tamim bin Hamad Al-Thani Hoto: picture-alliance/AP Photo/O. Faisal

Kasashen duniya da dama da suka hada da Faransa da Amirka da musamman kasar Kowaiti, sun dukufa wajen ganin an samu masalaha a tsakanin kasashen yankin na Golf, inda sarkin Kowaiti ke ta safa da marwa tsakanin kasashen Saudiyya da Daular Larabawa da Doha da nufin yayyafa wa wannan wutar rikicin diflomasiyyar ruwa tun kafin bakin alkalami ya kai ga bushewa. Ko da shi ke kasar ta Katar na ci gaba da samun goyon bayan kasar Iran da kuma Turkiyya a cikin wanann rikici, inda yanzu haka kasar Turkiyya ta sanar da shirin aike wa da sojojinta dubu uku a Katar a karkashin wata yarjejeniyar tsaro da kasashen biyu suka cimma a shekara ta 2014.