Wani mai jirgin ruwa ya faɗaɗa mulkin mallakar Jamus
April 2, 2024Yadda wani mai jirgin ruwa ya faɗaɗa mulkin mallakar JamusWane kamfani ne kamfanin na Woermann?
Da farko dai kamfanin jigila ta ruwa da harkokin kasuwanci, mai suna C. Woermann - daga Hamburg - ya fara buɗe kanti ne a Duwala na Kamaru a shekarar 1868. Ya yi harkokin kasuwanci ne a gaɓar tukun Afrika ta Yamma.
Adolph Woermann ya karɓi harkokin kasuwancin gidansu ne daga wajen mahaifinsa, wato Carl Woermann, a shekarar 1874. Wannan mai ƙwazo kuma matashi daga gidan Woermann ya yi imanin cewa Afrika wata kasuwa ce da za a sayar da kayayyaki da aka yi su da araha a Jamus, kamar barasa, sannan kuma waje ne da za a sami ma’aikata a araha don samar da kayan da za a sarrafa masu daraja a masana’antun Jamus.
Me ya sa Woermann ya matsa wajen samun wuraren da za a yi wa mulkin mallaka?
Ƙaruwar yankunan da aka mamaya da wasu ƙasashen Turai suka yi sai ya sa shi Woermann da sauran ‘yan kasuwar Jamus suka ji tsoron za su rasa ciniki a kasuwannin Afrika. Sannan kuma Shugaban gwamnati Otto von Bismack ba ya son kafa gundumomin don shimfiɗa mulkin mallaka saboda yana ganin hakan wani almubazzaranci ne.
Amma kamar yadda gasa tsakanin ƙasashen Turai wajen mamaye harkokin kasuwanci a Afrika ta ƙaru, haka ma kamun ƙafa ya ƙaru daga ‘yan kasuwa irin su Woermann. A shekrar 1883, sai ya bayar da shawarar a mallaki yankuna a Afrika Ta Yamma, ya kuma ja hankalin Bismarck cewa hakan zai nuna Jamus a matasayin ƙasar da ta isa.
Wane irin muhimmanci Woermann yake da shi a kan harkar mulkin mallaka?
Manyan masana tarihi sun gabatar da dalilai a kan cewa ƙasar Kamaru ba za ta zama mallakar Jamus ba, ba tare da taimakon Woermann ba. Yarjejeniyar Jamus da Duwala da aka ƙulla a watan Yulin shekarar 1884, wadda sarakunan Duwala Bell da Akwa suka sa wa hannu, ta ba wa Woermann ikon mallakar filaye da mamaye harkokin kasuwanci a Kamaru.
Woermann ya taka muhimmiyar rawa a Taron birnin Berlin na shekarar 1884/1885 wadda a nan ne aka tabbatar da duk wasu abubuwa da suka danganci ikon kafa mulkin mallaka na ƙasahen Turai. Wannan ya sa harkokin safarar jiragen ruwan Woermann
sun haɓaka, saboda kasancewarsa na hannun damar jagororin mulkin mallakar Jamus.
"Keɓaɓɓun Yankuna" suna da kyau ga ‘yan kasuwa saboda sun bayar da kariya ga kamfanoni Jamus da kuma kasuwanninsu daga barazanar ƙasashen Turai. Sannan suna iya dogara da ƙarfin sojojin Jamus.
Me kamfanin Woermann ya sayar?
Kimanin kashi 60 cikin 100 na kayan da Jamus take fitar wa ƙasashen waje barasa ce, sai kuma makamai don bayar da kariya ga gundumomin mulkin mallaka daga turjiyar mazauna wuraren.
Wannan shi ya ba wa jami’an mulkin mallakar Jamus ƙarfin guiwar kutsawa ciki don su ci moriyar harkokin kasuwancin wuraren. A shekarar 1905, kamfanoni 200 ne suke harka a Afrika Ta Yamma, 30 na Woerman ne shi kaɗai. Sun noma kayan amfanin gona masu kawo kuɗi irin su kwakwar man ja da koko da roba da taba da kuma kofi a Kamaru, nesa da gaɓar teku.
Shin yarjejeniyar Jamus da Duwala ba ta hana wannan ba?
Sarakunan Duwala sun san cewa sun sa hannu a kan yarjejeniyar da ta taƙaita duk wani abu da Jamusawa za su yi a iyakar bakin teku. Amma jami’an mulkin mallaka sun gabatar wa da sarakunan wata takardar ta daban cikin Jamusanci, wadda ita aka sa wa hannun daga baya. Matsayin yankin ya ba wa kamfanionin Jamus dama su gudanar da harkokinsu tare da taimakon sojoji, don haka sai ga shi a hankali Duwala ta rasa ikon gudanar da harkokin kasuwancinta da kuma filayenta.
Ta yaya mulkin mallaka ya shafi mutanen Kamaru?
Shigar da kaya ya sa kamfanin Woermann ya sami riba mai yawa, yayin da hakan ya kashe harkokin tufafi da ƙungiyar ‘yan Kamarun ke yi, kuma yawancinsu ma ba su taɓa ji, ballantana ma su amince da wasu sharuɗa na Yarjejenitar Jamus Da Duwala ba.
An tilasta wa ɗaruruwan mutane maza da mata yin aikin ƙwadago a sababbin gonaki, inda babu yanayi mai kyau, ga kuma azabtarwa ba ƙaƙƙautawa.
Jami’an mulkin mallaka marasa Imani, irin su Jesko von Puttkamer sun tilasta wa ‘yan Kamaru guda 20,000 zuwa 30,000 noma da jigilar roba daga cikin ƙasar zuwa inda jiragen ruwa suke. An wulaƙanta sarakunan da suka nuna turjiya a bainar jama’a, an ƙona ƙauyuka, wanda hakan ya sa dole aka dinga yin gudun hijira zuwa garuruwan da suke ƙarƙashin Jamus.
Yayin da Rudolf Douala Manga Bell ya nuna turjiya, wanda shi ne babansa ya sa hannu a yarjejeniyar da aka yi tsakanin Jamus da Duwala a shekarar 1884, a kan cewa ana cin zarafin jama’arsa ana kuma ƙwace musu filayensu, sai nan take aka kama shi, aka kuma kashe shi a shekarar 1914.
Ta yaya mulkin mallaka ya shafi Namibiya?
Kamfanin zirga-zirga na Woermann shi kadai ya yi jigilar kimanin sojoji 15,000 zuwa Afrika Ta Kudu don su murƙushe turjiyar Herero da Nama a tsakanin shekarar 1904 da ta 1907. Kamfanin ya sami miliyoyin kuɗi wajen jigilar ma'aikata, da kayayyaki da kuma makamai na ƙasar Jamus. A wani lokaci kuɗin ya kai sama da kuɗin Jamus 600,000,000, adadi mai ban mamaki a lokacin, wanda Jamusawa masu biyan haraji suka tara.
Sauran ‘yan Nama da Herero kuma da suka tsira sai aka kai su kurkukun Swakopmund da Lüderitz, inda kamfanonin Jamus suke, waɗanda suka haɗa har da na Woermann, aka yi amfani da su a matsayin fursunonin yaƙi kuma leburori don yin aikace-aikace, kamar shimfiɗa titin dogo da aiki a gaɓoɓin teku.
Me ya faru bayan Jamus ta rasa gundumomin mulkin mallakarta a shekarar 1919?
Kusancin da kamfanin Woermann ke da shi da ƙasar Jamus ya sa ita Jamus ɗin ta rasa tasirin da take da shi a Afrika yayin da aka matsa mata da ta rabu da yankunan da take yi wa mulkin mallaka bayan Yaƙin Duniya na Farko. Zamanin cinikayya na kama karya irin na mulkin mallaka ya wuce, amma har yanzu al’ummun ƙasashen Kamaru da Namibiya suna da tabon illar haɗamar da aka yi da tashin hankalin da suka gani a lokacin.
DW ce ta shirya shirin waiwayen Mulkin Mallakar Jamus, Ofishin Kula da Harkokin Waje na Jamus (AA) ne ya ɗauki nauyi. Ƙwararru a ɓangaren tarihi da aka tuntuɓa su ne Farfesa Lily Mafela da Farfesa Kwame Osei Kwarteng da Reginald Kirey.