1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yadda 'Yan tawayen Siriya ke samun Makamai

February 19, 2013

Turai da Amurka na taka tsan tsan da muradin 'yan tawayen Siriya na bukatar a wadata su da Makamai da za su yaƙi Sojojin gwamnati.

https://p.dw.com/p/17hCR
Hoto: picture-alliance/dpa

 A dangane da hakane ma mahawarar tsawaita wa'adin takunkumin shigar da makamai zuwa cikin Siriyar ya mamaye taron ministocin harkokin waje na tarayyar Turai a birnin Brussels a wannan litinin.

Ministan harkokin wajen tarayyar Jamus Guido Westerwelle na daga cikin mafi yawan mahalarta taron da suka jaddada muhimmancin faɗaɗa wa'adin haramta shigar da makamai cikin kasar, domin a ganinsu hakan ba zai haifar da wani alfanu ba face ƙara tsawaita wannan rikici na yaƙin basasa da ƙasar ta tsinci kanta, wanda kuma tuni ya hallaka rayuka mutane masu yawa.

Takunkumin makamai dai yana taka rawa na siyasa, soji dama batu daya shafi al'umma ta fannin kabilanci.  Samarwa da 'yan tawayen Siriya makaia domin yaƙar gwamnati, batu ne da kasasahen yammaci ba zasu iya tunaninsa ba, domin hakan ba zai haifar da komai ba face ƙara tsananta zubar da jini tsakanin jama'a, kamar yadda Michael Brzoska Direkta a cibiyar nazarin zaman lafiya da harkokin tsaro na jami'ar Hamburg ya nunar.

Alltag der syrischen Rebellen
Hoto: Rob van Delft

Ya ce " A yanzu haka mummunan abu ne da Sojojin gwamnati ke amfani da manyan makamai. A yayinda su muka 'yan tawaye ke dogaro da kananan makamai da wasu da suke sarrafawa da kansu, hakan ma bai dace ba, amma ana iya cewar da sauki fiye da idan an ce su ma 'yan tawayen sun mallaki da muggan makamai".

To sai dai masu adawa da takunkumin shigar da makamai Siriyar na ganin cewar bawa 'yan tawayen makamai zai taimaka musu wajen samun nasarar murkushe mayakan gwamnati,kuma hakan ne zai kawo karshen wannan rikici.

Ƙwararre kan ƙasar  Siriya a  ƙasar Izraela Eyal Zisser na ganin cewar ya kamata a dubi wannan lamari da idon basira...

Ya ce" abun da ya dace ne ace Duniya ta taimakawa 'yan tawayen da makamai, kasancewar suna wakiltar wani ɓangare ne na al'ummar Siriya mafi girma, kuma dakarun gwamnati na ci gaba hallaka su. Dangane da hakane ya zamanto wajibi a ɗauki matakin da ya dace na kawo karshen wannan rikici".

Syrien Kämpfe Militärflughafen Menagh
Hoto: Reuters

To sai acewar Direktan cibiyar nazarin zaman lafiya na Jami'ar Hamburg Brzoska, tsarin hana shigar da makamai zuwa cikin Siriya daga ɓangaren Amurka, turai da wasu ƙasashe na fuskantar giɓi ko kuma kura krai masu yawa..

Ya ce " Saudi Arabiya da Katar suna samar wa 'yan tawayen tallafin kuɗi da makamai, kazalika Turkiyya dake makwabtaka babu masaniya dangane da irin tallafi da goyon bayan da take bawa 'yan tawayen na Siriya. A ƙasashe dake makwabtaka dilallai na cigaba da jibge makamai, alal misali a Lebanon wadda takan iya sayen makamai daga rigingimun baya. Kazalika suma sojojin Siriyan manyan dillalan makamai ne, kuma 'yan tawayen sun kai somame ma'ajiyar makaman kuma sun ɗiba. Zai iya yiwuwa akwai makami dake shiga hannun 'yan tawayen a hannun jami'an leken asiri, amma bayanai kalilan ne aka sani dangane da hakan". 

Ba'a fidda tsammanin yiwuwar kwararar wasu makamai zuwa cikin Siriya ta hannu kungiyoyin tarzoma na kasashen waje ba, musamman ma wadanda suke da masaniya dangane da yadda za'a sarrafa wasu makamai na yaƙi. Batu kuma da kwararre kan harkokin Siriya dake Izraela Zisser yace ba za'a iya fidda tsammanin yiwuwar amfani da irin wadannan makaman wataran akan turai ba. A ɓangaren gwamnati kuwa, an samu koma baya dangane da makamai da Siriyan ke samu daga Rasha, koda yake acewar Darektan cibiyar nazarin zaman lafiya Brzoska, har yanzu Siriya na samun makamai daga Rasha.

( Ana iya sauraron rahotannin daga ƙasa)

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita           : Yahouza Sadissou Badobi