Yadda za a kare kai daga cutar coronavirus
Mutane a duniya na amfani da abubuwan rufe baki da hanci domin kare kansu daga kamuwa da kwayar cuta coronavirus. Ko da yake akwai wasu matakai da suka fi inganci. Ga wasu shawarwari daga Hukumar Lafiya ta Duniya WHO.
Riga-kafi ya fi magani
Babu tabbacin ko abin rufe baki da hanci kamar a nan sama zai iya ba da cikakkiyar kariya daga kwayar cutar virus. Sai dai yana hana wasu kwayoyin cuta shiga baki ko hanci. Wani muhimmin abu shi ne, suna hana mutum taba bakinshi ko hanci (abin da mutane da dama ke yi a fakaice). Idan da ma kana ciwo to abin rufe baki da hanci zai hana wasu kamuwa da cutar ta dalilinka.
Wanke hannaye da ruwan magani
A jerin shawarwarin da ta bayar kan yadda za a kare kai daga kamuwa da kwayar cutar, Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ba ta ambato abin rufe baki da hanci ba. Abu mafi muhimmanci shi ne wanke hannu a kai a kai. Hukumar ta WHO, ta bayar da shawarar amfani da ruwan magani mai sinadarin alkohol wajen wanke hannu, kamar wanda ake gani a sama a wani asibiti.
Sabulu da ruwa ma za su biya bukata
Mataki mai sauki na yau da kullum shi ne ruwa da sabulu, idan akwai su a kusa. Sai dai a tabbatar an wanke hannu sosai da sosai.
Tari da atishawa- amma a yi abin da ya kamata!
Ga dai abin da likitoci suka ba da shawara: Idan ana tari da atishawa a yi amfani da cikin gwiwar hannu a rufe baki da hanci. Ko kuma a yi amfani da takardar tissue — amma a yar nan-take a kuma wanke hannu. Amma idan aka yi amfani da kayan sawa, ka da a yar da su. A rika wanke su a kai a kai ko kuma a kai wa masu wanki na zamani.
A guji wannan!
Ga wata shawara da watakila ba kowa ne za ta yi wa aiki ba: A guji zuwa kusa da mai fama da zazzabi da tari! Idan ta kama dole za a kula da masu jinya to a tabbatar cewa an dauki karin matakan kariya.
Kana zazzabi? To garzaya gun likita, amma ba yin balaguro ba!
Idan kana zazzabi ko tari ko wahalar yin numfashi, ka yi gaggawar zuwa neman magani wajen likita. A guji wuraren haduwar jama'a domin ka da wasu su kamu. Ka kuma yi wa likitanka bayani idan ka ziyarci wasu wuraren a baya-baya.
A guji taba su!
Idan aka shiga kasuwannin dabbobi a yankunan da yanzu ake fama da sabuwar kwayar cutar ta coronavirus, a guji taba dabbobi masu rai da kuma wuraren da aka ajiye dabbobin.
Barka da aiki — amma ba danye ba!
A dafa nama sosai. A guji cin danyen nama a kuma yi takatsantsan da shan madara ko kuma naman da bai dahu sosai ba. A yi takatsantsan wajen amfani da danyen nama da madara ko kayan ciki na dabbobi don kar a gurbata kayan abinci da ba a dafa ba. Wadannan su ne matakai kyawawa da za su taimaka wajen hana yaduwar cututtuka.