1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yahouza ya ce za su tattauna don cimma maslaha

Abdullahi Tanko Bala
April 19, 2017

Sabon ministan ilimi mai zurfi na Nijar Malam Yahouza Sadissou ya bayyana matakan da zai dauka don magance matsalolin yajin aikin malamai da zanga-zangar dalibai a kasar.

https://p.dw.com/p/2bVRN

Shugaba Mahamadu Issoufou na Jamhuriyar Nijar ya yi wani karamin gara- bawul ga gwamnatinsa a daren Talata zuwa Laraba inda aka tsige Malam Ben Omar Mohamed ministan ma'aikatar ilimi mai zurfi daga kan mukaminsa tare da maye gurbinsa da Malam Yahouza Sadissou. Tsige Minista Ben Omar daga kan mukaminsa na daga cikin bukatun da kungiyar dalibban kasar Nijar ta gindaya wa gwamnatin kasar domin komawa kan tebirin tataunawa biyo bayan kisan wani dalibi lokacin zanga-zanga.

Ko me sabon ministan ilimi mai zurfi Yahouza Sadissou zai yi domin daidata al'amura a jami'o'in Nijar?