1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An zargi tsohon shugaban kasar Gambiya da yin lalata da mata

Abdoulaye Mamane Amadou
June 26, 2019

Kungiyoyin kare hakin bani Adama sun zargi tsohon shugaban Kasar Gambiya Yahya Jammeh da laifin yin lalata da mata a yayin da yake kan iko, inda yayi amfani da karfin iko uzurawa mata.

https://p.dw.com/p/3L7jb
Gambia Yahya Jammeh
Hoto: imago/UPI Photo

Kungiyar Kare Hakkin bil Adama ta Human Rights Watch ta zargi tsohon shugaban Kasar Gambiya Yahya Jammeh da aikata laifin muzgunawa wasu mata ta hanyar karfi da yaji don yin lalata da su. A wani rahoton da ta wallafa  a kasar Senegal, kungiyar ta ce ko baya ga karfin tuwo tsohon shugaban yayi amfani da karfin ikonsa da ma kudi don uzurawa matan a lokacin da yake kan madafan iko, abin da lauyan kungiyar ta kare hakkin dan Adam din ya ce dukkaninsu miyagun laifuka ne da ake iya sa a hukumta Jammeh a kansu domin kuwa bai fi karfin doka ba.