Yajin aikin likitoci a Adamawa da ke Najeriya
October 3, 2013Yajin aikin da ya shiga rana ta uku ya sanya marasa lafiya da ke kwance a asibitocin gwamnati yanke shawarar barin asibitocin saboda rashin likitocin da za su kula da lafiyarsu, yayin da wasu ke cigaba da zama suna samun taimakon da ba a rasa ba da jami'an jinya.
Majinyata da ke da manya larurori dai su ne wannan matsala ta fi shafa musamman ma dai masu karamin karfi. A dangane da wannan hali da ake ciki ne dai wakilinmu na Yola Muntaka Ahiwa ya zanta da wasu marasa lafiya da ke asibitin gwamnatin tarayya da ke Yola, fadar gwamnatin jihar ta Adamawa inda suka tabbbatar da cewar yajin aikin likitocin ya jefa su cikin tashin hankali.
Majinyatan dai sun kira ga gwamnatin da ta taimaka ta sanya baki a cikin lamarin don likitocin su koma bakin aikinsu. Shi ma dai wani da ya ke jinyar mahafinsa cewa ya yi ya kyautu likitocin da gwamnati su sasanta ko a samu sararin kulawa da mutane da ke cikin wani hali don gudun kada a kai ga samu asarar rayuka.
To a daidai lokacin da majiyatan da masu kula da su ke godon gwamnati da likitocin su daidaita, likitocin na jihar ta Adamawa sun ce wannan mataki da suka dauka na yajin aiki wata hanya ce ta ganin gwamnati ta tashi tsaye wajen inganta yanayin aikinsu bayan ga yunkuri na ganin an biyasu hakkokinsu da suka makale.
Dr. Habila Ibin shi ne shugaban likitoci masu da ke kan hanyar kwarewa a fannonin aikinsu daban-daban wata Association of resident doctors reshen asibitin gwamnatin tarayya da ke Yola, ya ce tunda aka fara shirin horas da likitoci a kasa ba a taba zama an gindaya wata ka'ida game da koyar da likitoci masu bukatar kwarewa ba baya ga batun rashin biyan wasu likitocin hakkinsu yadda ya kamata a karshen wata.
Kawo yanzu dai gwamnatin jihar ta Adamawa ba ta ce komai ba game da wannan batu wanda jama'ar jihar ke cewar in aka cigaba da tafiya a matsayin da ake to rayukan marasa lafiya a jihar za su cigaba da kasancewa cikin barazana.
Mawallafi: Muntaka Ahiwa
Edita: Mouhamadou Awal