Yake-yaken basasa sun karu a wannan karni
June 18, 2018Kungiyar agajin kasa da kasa ta Red Cross ta ce adadin yake-yaken basasa ya nunka sama da sau biyu daga farkon wannan karni, lamarin da ke barazana ga makomar fararen hula da dama da kuma haddasa sabbin kalubale ga kungiyoyin agaji na duniya.
Kungiyar ta bayyana hakan ne a cikin wani rahoton bincike da ta wallafa a wannan Litinin inda ta ce a shekaru shida da suka gabata an samu karuwar kungiyoyin mayakan sa kai masu dauke da makamai fiye da a shekaru 60 da suka gabata, abin da sanya kuma ake fuskantar wahala wajen shawo kan mayakan ga kiyaye tsarin aikin kungiyoyin agaji.
Rahoton ya ce adadin kungiyoyin da ke fada da juna a cikin rigingimu ya canza sosai inda a yanzu haka kaso daya daga cikin uku na yake-yaken da ke gudana ne kawai ake samun bangarori biyu na fada a yayinda ake samun kungiyoyi tsakanin uku zuwa tara a cikin rikici guda a yau.
Rahoton ya ce a watan Oktoban 2011 an lissafa kungiyoyi 236 na mayaka a birnin Misrata na kasar libiya a yayin da aka kididdige kungiyoyin mayaka sama da 1000 a yakin Siriya a 2014.