Yaki da cin hanci tsakanin malaman Nijar
January 17, 2017
Rangadin ya zo ne a dai dai lokacin da gwamnatin Jamhuriyar Nijar ke cewar ta
cika alkawalin malaman da ta dauka na biyansu kudaden alawus din albashi da suke bin ta.
Kungiyar malaman ta ce wasu daga cikin hukumomi na amfani da HALCIA wajen tursasa ma magoya bayansu a karkara. Zargin na zuwa ne a rana ta biyu da fara aikin tantance malaman da tawagar hukumar ke gudanarwa a yankin na Damagaram da ke kumshe da malaman da ke karantarwa a karkashin tsarin kontragi sama da dubu 10 ya fara shan karo da martanin kungiyar malaman. Sakatarenta Ya'u Abdu ya bayyana cewar ba zasu taba amincewa da matakin ba.
A shekarar da ta gabata ma dai an gudanar da aikin tantance malaman kontragin wanda daga bisani aka gano an tabka kurakura ba na wasan yaro ba inda a yanzu gwamnati ta dauki dukan matakan tsabtace aikin. Ita ma dai kungiyar iyayen yara matsalar tabarbarewar ilimin na cimmata tuwo a kwarya.