1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

An kafa dokar kulle a Afirka ta Kudu

Abdoulaye Mamane Amadou
June 28, 2021

Hukumomi a Afirka ta Kudu sun dauki matakin hana tarukan jama'a, da rufe wuraren sayar da barasa har na tsawon makonni biyu, a wani mataki na dakile yaduwar sabon nau'in corona mai saukin yaduwa Delta.

https://p.dw.com/p/3veyw
Südafrika | Cyril Ramaphosa
Hoto: UNTV/AP/picture alliance

A jawabinsa ga 'yan kasar ta kafar talabijin, Shugaba Cyril Ramaphosa, ya ce kasar za ta kara daukar wasu kwararan matakai masu tsauri don dakile cutar, duba da yadda ma'aikatan jinya ke ta fadi tashin ceto rayukan jama'a a yayin da a share daya dakunan kwana na marasa lafiya ke kara karanci.

Tuni dai aka tsawaita dokar kulle a kasar wadda aka kakaba tun da jimawa, kana kuma ana hasashen sake rufe makarantun boko a wannan Jumma'ar, a yayin da alkaluma suka tabbatar da kamuwar mutane fiye da dubu 15 da suka harbu da sabon nau'in cutar samfurin Indiya.

Wannan matakin na zuwa ne a yayin da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta bayyana cewar yanzu hakan cutar ta karade kasashe akalla 85 na duniya.