Jamhuriyar Nijar: Yaki da cutar tamowa
May 7, 2024Talla
Hukumar Kula da Kididdigar Tattara Bayanai ta Jamhuriyar Nijar INS, ta shirya wayar da kan ne a birnin Damagaram ga hukumomi da jami'an kiwon lafiya da ilimi da gidan gona da kuma kafofin sadarwa. Hukumar ta dauki wannan matakin ne domin rage kaifin matsalar da ka iya mayar da hannun agogo baya wajen yaki da cutar, a daidai lokacin da farashin kayan abinci ke ci gaba da yin tashin gauron zabi a fadin kasar tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi. Wannan dai shi ne karo na biyu da hukumar ta INS ke shirya irin wannan wayar da kan, bayan wanda ya hada wakillan jihohin Tillabery da Yamai da aka gudanar a Yamai din fadar gwamnatin Nijar a kokarinsu na cimma matsayar yakar cutar a matakin kasa.