Yaki da nuna wariya da kyama ga Zabiya
June 14, 2023Shin kun taba cin karo da wannan kalma ta zeru-zeru da harshen Swahili? kalmar dai na nufin fatalwa Inda ake alakanta masu dauke da wannan lalura ta zabiya a Tanzania da wannan kalma. Abin takaici a kasar shi ne al'umma sun yi wa masu lalurar mummunar fahimta cewa su aljannu ne ko kuma wasu mutane na daban harma da amannar cewa ana amfani da sassan jikinsu wajen tsafi domin a yi kudi, wanda har yanzu a kimiyyance likitoci sun kasa warware wannan dambarwa a Tanzania.
Masu wannan larurar na zama cikin zulumi inda suke fafutukar neman maganin da zai sauya musu launin fata domin kaurace wa farmaki, inda guda daga cikin masu fama da lalurar Yohane Bahame, ya ce suna sayen man shafawa na akalla dalar Amurka 13, wanda da yawa daga cikinsu ke fuskantar kalubalen sayen maganin saboda matsalar tsadar rayuwa.
"Ya ce a tsari na zamantakewa a Tanzaniya, babu fahimtar juna game da masu fama da lalurar ta zabiya, wanda hakan ke haifar da fargaba a tsakanin al'umma. Kai babban abin da muke bukata shi ne batun samun kudin sayen man kula da launin fatar cikin sauki. Duk da wasu daga cikin kungiyoyi masu zaman kansu na tallafa wa zabiya, duk da haka galibi basa iya samun wannan tallafi."
Wata kungiya da ke tallafa wa zabiya mai suna ‘'Under the Sun'' ta gudanar da bincike tare da fitar da rahoton cewa a duk yara ‘yan kasa da shekara 10 a kasashen kudu da hamadar sahara masu fama da lalurar zabiya na fama da cutar daji wato cancer kuma kaso biyu cikin dari ne ke haura shekaru 40 a raye
Dr. Anna Henga, ita ce babbar daraktar hukumar kare hakkin dan Adam ta Tanzania, ta ce zabiya na cikin zullumi..
"Ta ce duk da yunkurin kare zabiya, ana ci gaba da kai musu mummunar farmaki, da hakan ke sanya fargaba, akalla an kashe zabiya biyu tsakanin shekara ta 2021 da 2022, kazalika an kuma samu wannan matsalar a wasu kasashe. Akwai bukatar a kafa kwamiti mai karfi na kare wadannan mutane masu rauni, musamman a lokacin gudanar da zabbuka da al'amura ke kara tabarbarewa da kuma yawaitar kai hare-haren ta'addanci".
Maduhu William, lauya ne kuma guda daga cikin masu fafutukar kare hakkin dan Adam a kasar Tanzania, ya ce zabiya na fama da cututtuka da ake alakanta su da camfe-camfe a kasahen nahiyar Afrika. Kazalika, matsalar kudin man da za su shafa domin rage musu radadin lalular wani abin tashin hankali ne.
"Ya ce Tanzania ta gabatar da dokoki da kudurori harma da tsare-tsaren da za su kare masu fama da lalurar, musamman dokar shekara ta 2010. A halin yanzu ana samun sauki dangane da wannan matsalar ta cin zarafin zabiya, godiya ta musamman ga masu ruwa da tsaki da suka yi fadi-tashin kare hakkin zabiya ta hanyar wayar da kan al‘umma cewa zabiya mutane ne kamar kowa".
A kowacce shekara akan gudanar da gangamin yaki da cin zarafin zabiya, domin fadakar da al'umma kan kare mutunci da yancin masu fama da lalurar. A kasar Tanzania, masu ruwa da tsaki kan wannan lalurar sun hadu a yankin Ruvuma da ke kuduncin kasar domin fidda matsaya kan kare martabar zabiya.