1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaki da zazzabin cizon sauro a kasar Nijar

Abdullahi Tanko Bala
April 25, 2023

Taken ranar ta wannan shekara shi ne lokaci ya yi da za a kawo karshen kamuwa da kwayar cutar Malaria

https://p.dw.com/p/4QXVu
DW Premium News | Thumbnail | Could climate change exacerbate malaria?
Hoto: DW

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta nanata cewa aiwatar da matakai na kawo karshen wannan cuta ya zama wajibi. A Jamhuriyar Nijar dai sannu a hankali kwaliya na biyan kudin sabulu dangane da matakan da hukumomin kiwon lafiya suke dauka na yaki da cutar ta Malaria.

Moskitoschutz in Togo
Hoto: picture alliance/Photononstop

Mata musamman masu juna biyu da kananan yara su ne suka fi fuskantar matsalolin cutar zazzabin cizon sauro, kuma suma da kansu sun ce a yanzu lamura sun sauya domin ana ganin alfanun matakan yaki da wannan cuta a cewar Hajiya Amina, wakiliyar mata a garin Junju.

A can ma yankin jihar Tillabery inda ake da kogin isa, yanki ne da aka dade ana kokuwar ganin an ciyo kan cutar zazzabin cizon sauro kuma babban mataki na gidan sauro mai dauke da magani da ake raba wa mata kyauta da ma sauran magunguna, na taimakawa sosai. Madame Soumana Safiyatou Kindo, ita ce shugabar kungiyar mata ta CONGAFEN reshen jihar Tillabery.

Symbolbild Malaria | Mücken
Hoto: Jonathan Nackstrand/AFP

Sai dai tun da jimawa an yi ta zancen samun allurar rigakafgin cutar ta Malaria wadda har yanzu wasu ke ganin cewa zancen tamkar shaci fadi sai dai an gani. Dr ibro Kane, shi ne Sakataran kasa na kungiyar jami'an kiwon lafiya da ayyukan jinkai ta SUSAS.

Abin jira a gani dai shi ne ko mafarkin yadda aka kawo karshen wasu cutuka da a baya suka addabi jama'a, a ga cewa ita ma wannan cuta ta Malaria mai saurin kisa ta zamanto tarihi a kasashen Afirka inda ake fama da ita.