Rayuka na salwanta a Zirin Gaza
October 27, 2023Ma'aikatar lafiyar Falasdinu ta ce ya zuwa yanzu mutane dubu 7.326 ne suka mutu tun bayan kaddamar da farmakin ramuwar gayya da Isra'ila ta yi kan kungiyar Hamas mai iko da Zirin Gaza.
Karin Bayani : Harin bam ya haddasa mace-mace a asibitin Gaza
Rundunar tsaro Isra'ila ta kai wasu jerin hare-hare ta kasa har a kwaryar Zirin Gaza, tare da rakiyar jiragenta na yaki ciki har da marasa matuka, kana rundunar ta ce dakarunta sun yi nasarar komawa gida bayan kutsen ba tare da ko kwarzane ba.
Ita kuwa Amurka na nazari kan yiwuwar kakaba wa Kungiyar Hamas da Iran wasu jerin sabbin takunkumai, wanda ke zaman wani sabon babi na rikicin da ke daukar salo.
Karin Bayani : Zirin Gaza: Goyon baya daga Larabawa
Majalisar Dinkin Duniya dai ta yi gargadin yiwuwar samun karin mamata a Zirin Gaza nan ba da jimawa ba samakaon mamayar da Isra'ila ke yi wa yankin tare da kiran da a gaggauta shigar da kayayakin agaji ga mabukata.