Yakin neman zabe ya fara gudana a kasar Kwango
November 19, 2023Kusoshi daga bangaren 'yan adawa sun fara zaburar da magoya bayansu, yayin da shugaba Félix Tshisekedi da ke neman wa'adi na biyu ke tallata ci-gaban da ya samar a fannoni da dama. Baya ma ga manyan tarurruka da bayyana a kafafen yada labarai da maka fosta don tallata manufofinsu da 'yan taka ke yi, Félix Tshisekedi ya shirya gudanar da gangamin siyasa a filin kwallon kafa na Kinshsa, yayin da daya daga cikin manyan masu kalubalantarsa Martin Fayulu ya nufin wani lardin da ke makwabtaka da Kinshasa don fara yakin neman zabe.
Karin bayani: Rajistar 'yan takarar shugaban kasa a Kwango
A ranar 20 ga watan Disamba ne, masu jefa kuri'a kusan miliyan 44 za su zabi shugaban kasa da 'yan majalisar dokoki da gwamnonin da shugabannin kananan hukumomi da kansaloli na Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango. Tuni ma hukumar zabe (Céni), ta ce ta kuduri aniyar shirya sahihan zabukan, duk da kalubalen jigilar kayan aiki da za ta iya fuskanta saboda fadin kasar Kwango da karancin ingantattun hanyoyi.