Yakin Ukraine na kara fargaba kan abinci
March 22, 2022Talla
Yayin da farashin mai da alkama suka yi tashin gwauron zabi kasashe da dama na fargabar aukuwar karancin abinci a daidai lokacin da ake cigaba da gwabza yaki tsakanin kasashe biyu da suka yi fice wajen noma abinci a duniya.
Tun bayan da Rasha ta dakatar da fitar da alkamarta zuwa kasashen waje, farashin alkamar ya yi tashin gwauron zabi. Kasashe da dama sun fara baiyana fargabar aukuwar yunwa da kuma zanga zanga sakamakon karancin abinci.
Martin Häusling mai magana da yawun jam'iyyar Greens a majalisar dokokin turai kan manufofin ayyukan gona yace dakatar da fitar alkama zuwa kasashen waje, tamkar Putin na amfani da abinci ne a matsayin makami yana mai cewa karancin abincin zai fi shafar kasashe matalauta.