Yakin Ukraine ya janyo tsadar abinci a Nijar
March 21, 2022Kasar Turkiyya wadda ta kasance daya daga cikin masu shiga tsakanin ta nuna fata bisa cewa an yi kusa cimma shirin tsagaita wutsa tsakanin bangarorin biyu na Rasha da Ukraine. Yayin da ake ci gaba da neman hanyar kawo karshen wannan yaki da ya haifar da milyoyin 'yan gudun hijira, Shugaba Volodymyr Zelenskyy na kasar ta Ukraine ya bayyana a wani faifan bidiyo da ya nunar da irin asarar da Rasha ke ci gaba da fuskanta yana mai cewa: "Toshe Mariupol zai shiga kundin tarihi a matsayin laifin yaki. Masu mamaya wannan birnin sun aikata ta'addancin da za a ci gaba da tunawa shekaru daruruwa masu zuwa. Kuma yayin da 'yan Ukraine ke shaida wa duniya halin da ake ciki, haka zai taimaka kan karin samun taimako. Yayin da Rasha ke kara ta'addanci a Ukraine, haka Rasha ke ci gaba da fuskantar sakamakon irin abin da ta shuka."
Rasha a sake yin barazanaryin amfani a makamaimasu linzame
A wuraren da aka yi dauki ba dadi tsakanin sojojin Rasha da na Ukraine masu kare biranen kasar, an nuna hotunan irin sojojin Rasha da aka kashe lokacin gumurzu. Sai dai tuni Rasha ta bayyana sake amfani da makami mai linzani na musamman tare dagewa ta lalata kayayyakin yakin kasar ta Uraine, Igor Konashenkov mai magana da yawun ma'aikatar tsaron Rasha ya yi karin haske:
"Sojojin Rasha suna ci gaba da aikin da suke yi na aikin soja na musamman. Kuma makami mai linzami da muka harba ya lalata runbun ajiye kayayyakin soja na Ukraine na karkashin kasa a wani kauye da ke yankin Ivano-Frankivsk."
Amirka da sauran kasashen duniya na taimaka wa Ukraine
Amirka tana cikin manyan kasashen duniya da ke taimakon Ukraine da makamai na zamani domin dakile kutsen da Rasha ta kaddamar. Shugaba Joe Biden na kasar ta Amirka ya ce taimako yanzu aka fara kuma nasara na bangaren wadanda suke kare kansu:
"Amirkwa sun amsa kiran Shugaba Zelenskyy na Ukraine bisa karin taimako, karin makamai da Ukraine za ta kare kanta, domin fada da 'yan mamaye na Rasha. Wannan shi ne abin da muke yi. Gaskiya, mun fara taimakon Ukraine tun kafin fara wannan yakin, lokacin da suka fara atisaye a kan iyakar Ukraine, abin da Rasha ta fara a watan Maris na shekarar da ta gabata. Mun dauki barazanar Putin na kaddamar da kutse da gaske. Mun kuma dauki mataki a kai."
Shi dai Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya ba da umurnin kaddamar da wannan kutsen. Sannan shugaban na Amirka ya yi amfani da karfin ikonsa wajen ci gaba da samar da kundin da Ukraine take bukata na kare kanta daga kutsen da Rasha ta kaddamar.