1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yakin Ukraine zai kwashe shekaru

June 19, 2022

Jagororin kasashen yamma, sun ce alamu na ci gaba da nuna cewa rikicin Rasha da Ukraine zai dauki lokaci mai tsawo duk da irin illolin da matsalar ke haddasawa.

https://p.dw.com/p/4Cupx
Großbritannien Rückkehr Boris Johnson Ukraine
Hoto: Joe Giddens/AP Photo/picture alliance

Shugabannin kasashen yammacin duniya, sun ce alamu na ci gaba da nuna yadda yakin da Rasha ta kaddamar a Ukraine zai iya daukar shekaru ba tare da an kawo karshen sa ba.

Sakatare Janar na kungiyar ta NATO, Jens Stoltenberg tare da Firaministan Birtaniya Boris Johnson su ne suka bayyana hakan.

Stoltenberg ya ce dole ne kasashe su ci gaba da hada karfi saboda illar rigimar ke jaza wa duniya baki daya, musamman na karancin makamashi da kuma abinci da ake gani a yanzu.

Kalaman shugabannin biyu dai sun zo ne a lokacin da Rasha ke tsananta kai hare-hare a gabashin Ukarine bayan amincewar da kungiyar Tarayyar Turai ta yi na shigar da Ukraine a cikinta.

Firaminista Boris Johnson ya ce komi tsadar tallafi ga Ukraine a wannan yakin, dole ne a dore a kan hakan.