An yi ganawar 'yan adawa a Jamhuriyar Nijar
June 10, 2022A Jamhuriyar Nijar a karon farko tsohon shugaban kasa Mahamane Ousmane kuma wanda ya fafata a neman shugabancin kasar tare da Shugaba Mohamed Bazoum, ya bayyana a gaban sauran jagororin 'yan adawa na kasar inda ya yi bayani tare da fadin dalillansa na daukan wasu matakai da suka kauce wa kasar fadawa a wani sabon rikici na siyasa da ba sa inda zai kai kasar ba.
Karin Bayani:Nijar na bukatar tallafi a fannin tsaro
Fitowar ta tsohon shugaban kasa Alhaji Mahamane Ousmane, da aka jima ana jira har ma daga bangaran masu mulki ta kasance mai kumshe da darusa masu tarin yawa, inda tsohon dan takarar ya ce bayyana tarin matsalolin da kasar ta Nijar ke fuskanta sakamakon shekaru kimanin 10 da aka shafe ana gudanar da mulki na danniya da baba-kere wanda hakan ya sanya ya yi iyakar kokarinsa na kaucewa kasar ta Nijar wani sabon tashin hankali na siyasa duk kuwa da cewa da dama daga cikin abokan tafiyarsa ba su so hakan ba.
Tuni dai masu sharhi kan harkokin siyasar Jamhuriyar Nijar da ma ta duniya irin su Malam Sani Rourai na ganin cewa duk da cewa idan ba su sake wani salon a tafiya ba, to makomar 'yan adawa a kasar babu wani tabbas.
Za a iya cewa babban abin da za a lura da shi da kuma masu nazari tuni suka amince da shi, shi ne na ganin a tare da tsohon shugaban kasar da ma 'yan adawa baki daya akwai matasa masu ilimi da kuma suke da akida ta kawo sauyi dan ganin kasar ta bi ta farki mai kyau na dimukuradiyya. Kane habibou Kadaure shugaban jam'iyyar SDR Sabuwa na da ga cikinsu wadannan jagorori matasa na adawa.
Abin jira a gani dai shi ne na irin kokowar da 'yan adawa za su fito nan gaba a kasar da kungiyoyin fararan hula da kansu ke kokawa da tauye musu hakki na zanga-zanga ko wani jerin gwano wanda suka ce akasari ana labewa da guzuma ne domin a harbi karsana a dimukuradiyyar ta Jamhuriyar Nijar wadda daga waje tafi samun yabo.