1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Zimbabuwe tana takura 'yan adawa

March 24, 2022

Kungiyoyin kare hakkin da adam da suka hada da Amnesty Internetional na nuna fargaba kan yadda 'yan jam'iyya adawa a kasar Zimbabuwe ke fuskantar barazana biyo bayan mutuwar mambobin jam'iyyar biyu.

https://p.dw.com/p/48ymE
Simbabwe | Polizeieinheiten vor einem Gebäude der Opposition in Harare
Hoto: picture-alliance/AP Photo/T. Mukwazhi

 

'Yan adawa dai a kasar ta Zimbabuwe na nuna shakkunsu ne tun bayan da wasu tawaga dauke da adduna da mashi suka kai hari ga magoya bayan jagoran adawar kasar Nelson Chamisa. Harin da yayi sanadiyar mutuwar mutane biyu yayin da wasu 22 suka jikkata. Robert Shivambu na kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International na cewa hakan ya saba tsarin siyasa.

Gabanin harin da aka kai dai, mataimakin shugaban kasar Zimbabwe na mai cewa jam'iyya mai mulki ta ZANU-PF za ta murkushe jam'iyyar adawa ta kasar. Kalaman da suke haifar da cece-kuce a kasar tare da kalubalantar shugaban da ake ganin tamkar yana tunzura magoya bayan jam'iyyarsa ne suka kai hari ga bangaren adawa. kungiyar Amnesty na daga cikin wadanda suka ga wallen kalaman.

Tuni dai jami'an 'yan sanda suka ce sun kame gomman magoya bayan jam'iyya mai mulki a kasar da ake zargin suna da hannu a kitsa harin.

red beret - July 28 2018 Harare Harare ZImbabwe 28 07 2018 Supporters of the opposition MDC Alliance pres
Hoto: imago/ZUMA Press/M. Baloyix

Ana dai ganin tamkar an kashe maciji ne ba a sare kanshi ba a yayin da kasar ta Zimbabuwe za ta gudanar da zabukan fidda gwani a karshen wannan watan, kuma ana ganin rikici na kara kunno kai gabanin zaben. Wani dan adawa a kasar Last Maengehama da ya taba fadawa komar 'yan sanda suka kuma mi shi duka a zamanin mulkin tsohon shugaban kasar marigayi Robert Mugabe ya dora alhakin rikicin siyasar kasar kan gwamnatin Shugaba Emmerson Mnangagwa da kuma jam'iyyarsa da suke amfani da dabaru wajen kawo karshen 'yan adawa.

Zaben fidda gwanin da za a gudanar a wannan wata dai zai kasance sharar fage ga lamuran babban zaben kasar da za a gudanar a badi.