Yan adawa sun koka kan yanayin mulki a Nijar
November 14, 2013
Kawancan 'yan adawar na ARDR, ya bayyan haka ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis a birnin Yamai. Sai dai bangaran jam'iyyun da ke milki ya musanta wadannan zarge-zarge, tare da bayyana 'yan adawar a matsayin wadanda su ka rude tun bayan kayen da su ka sha a majalisar dokokin kasar dama a
majalisar kansalolin birnin Yamai.
Sanarawar wacce ita ce ta farko da kawancan jam'iyyun adawar na ARDR ya
fitar tun bayan kafa shi yau kusan wata daya da rabi, ya samu halartar
shugabannin yan adawar da su ka hada da Alhaji M. O. da Malam Hamma
Amadu da kuma Alhaji Seini Omar na jam'iyyar MNSD NASARA. A cikin
sanarwa tasu kawancan jam'iyyun adawar na ARDR ya yi korafe-korafe da
dama dangane da yadda masu milkin kasar ta Niger na yau ke tafiyar da
shi. Daya daga cikin korafin da 'yan adawar su ka yi shine na zargin
shugaban kasa da nuna bangaranci dama kabilanci a cikin tafiyar da
milkinsa, wanann kuwa a sakamakon wasu kalamai da ya furta lokacin wata
ziyara da ya kai a cikin jaharsa ta haihuwa. Alhaji Dudu Rahama shine
kakakin kawancan jam'iyyun adawar na ARDR:
Shugaba Isufu ya tafi Tawa ya ce dan karamin gatarinka ya fi sari ka
bani. Kasar nan idan mu ka shiga cikin wani hali na banbancin jaha, na
banbncin jini, na kabilanci mun shiga wani hali to kuma wanann
gwamnatin ita za ta samu ciki. A matsayinsa na shugaban kasa ya zo
garinsu ya ce guntun gatarinka ya fi sari ka bani hadari ne, domin shi
ai wakilin talakawa ne, shugaba ne na kasa wanda ya kamata kar ya zamo
ba guntun gatarin wani ba ne shi dan shi guntun gatarin kasa ne gaba daya.
To saidai da ya ke mayar da martani akan wanann zargi Honnorable
Shafiou Magaria na jam'iyyar PNSD Tarayya mai milki cewa ya yi zargin
'yan adawar ba shi da tushe kuma ma rashin ta fadi ce kawai.
Ba su ta cewa ne domin in ka duba wadannan shugabannin guda ukku da
shi shugaban CDS da na Lumana da na MNSD ba wani daga cikinsu wanda ya
gina wani abu da kudinsa domin amfanin alummasu wadda ta ke zabensu
kuma tsammahani su ke har yanzu kan yan kasa bai waye ba. Yanzu ko 'yan
kasa sun gani cewa wannan mutuman bai muna komi ba sai wannan
fituntunun ya ke so ya hada balle ma in ka duba abubuwan da su ka faru
anan makobtammu Najeriya a bisa batun kabilanci ya isa darasi.
Wani zargi na biyu da yan adawar su ka yiwa shugana kasa da
gwamnatinsa shine na yada tabi'ada cin hanci da rashawa a cikin kasar,
suna masu bada misalin da abun da ya wakana a majalissar dokoki dama a
majalissar mashawarta ta birnin yamai, kamar dai yanda za ku ji karin
bayani daga Alhaji Dudu Rahama Kakakin kawancan adawar na ARDR.
Abun da ya wakana a cikin zauran majalissa da a cikin karamar hukumar
yamai inda kansaloli ake sayansu da kudi muna da shaidar farko wanda
su ka kawo kudi a jam'iyyar Lumana su ka ce ga kudin da aka basu dan su
kada Omar Dogari yau depute ya zamo kamar a zo kasuwa asaya kaza ko
akuya muna da hujjoji kuma diptoci sun fito a bangaran adawa da
majarity sun ce an saye diptoci.
Akan wanann zargi ma dai Honnorable Shafiou Magaria na jam'iyyar ta PNDS
Tarayya mai milki ya mayar da martani kamar haka:
Ni gani na ke nuna kasawa ne ga wanann kawance na yan adawa domin ai
ba yau ba mu PNDS Tarayya ke kada majority akan muna mu kadan kuma
ina ganin shi shugaban majalissa na yau ya san ko mi kenan to a
lokacin ann muna adawa shima kuma kudin mu ka bada?kuma wanann sanarwa
dan dai kar a ce ba bu su ne wato bari mu motsa dan kar a ga kamar
wanann gwamnatin ta mirje mu, kuma dole ne ko suna so ko ba sa so doli
ne gaskiya ta mirje karya wanann kuma ai ba yau ba aka fara.
Za a iya cewa sannu a hankali rikicin siyasar da ya taso a Nijar tun
bayan kafa gwamnatin hadin kan kasa ya jefa yanayin syasar kasar ta
Nijar a cikin wani yanayi da ya yi daidai da wani karin magana da ke
cewa kuda ya ce su baba an tafi kasuwa dawowarta gida sai dai Allah.
Mawallafi: Gazali Abdou Tasawa
Edita: Umaru Aliyu